Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Alkali

Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Alkali

  • Gwamna Masari na Katsina ya kalubalanci Sifeto Janar na yan sanda kan lamarin tsaro
  • Masari yace yan sandan Najeriya basu da makamai na kwarai don yakan yan bindiga
  • IGP Alkali yace suna shirin daukan sabbin yan sanda 20,000

Katsina - Gwaman jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi ikirari hukumar yan sanda ba tada isasshen jami'an da zasu samar da tsaro kan jiha mai adadin mutane milyan takwas.

Masari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Sifeto Janar na yan sanda, Alkali Usman Baba, a gidan gwamnatin jihar, ranar Alhamis, DailySun ta ruwaito.

Masari yace babu isassun yan sandan da zasu iya bada tsaro a jihar Kastina.

A cewarsa:

"Jihar Katsina na da mutane kimanin milyan takwas amma yan sanda nawa muke da shi a Katsina.?"

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

"A nawa lissafin na adadin yan sandan dake kananan hukumominmu, ban tunanin muna da yan sanda 3,000 a jihar."
"Misali sun kai 3,000, hakan fa na nufin kowani dan sanda daya na kare mutane 200,000. Ta yaya zai iya aiki?"

Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Alkali
Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Hoto: KTSG
Asali: Twitter

Yan sanda basu da isassun makamai, Masari

Masari ya kara da cewa jami'an yan sandan Najeriya basu da isassun makamai ko da tsofaffi ne ballantana sabbin makaman zamani.

Ya ce wannan shine abinda ake ciki a dukkan sauran hukumomin tsaron Najeriya.

Yace:

"Idan akayi maganar makamai kuma, me yan sanda ke da shi? Idan aka zo kan maganar sabbin makamai, nawa yan sanda ke da shi?"
"A nan, yan bindiga sun fara baiwa matasa N5,000 da kwayoyi don shiga aikin barandanci."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

IGP Baba ya bayyana yadda ya zama shugaban yan sanda a mawuyacin lokaci

Sufeto Janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya ce ya karbi ragamar jagorancin rundunar a wani mawuyacin lokaci.

Da yake magana lokacin da ya ziyarci Gwamna Bello Masari na Katsina, Baba ya bayyana wasu kalubalen da rundunar ke fuskanta.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin 'yan sanda 20,000 don inganta karfin rundunar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng