Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a
- Shigar da Kashim Shettima yayi zuwa taron NBA inda ya wakilci Tinubu, ya dauka hankulan ma'abota amfani da soshiyal midiya
- An ga Shettima ya bayyana sanye da kwat inda ya cike gayunsa da takalman motsa jiki, lamarin da yasa wasu suka zargesa da rashin iya saka kaya
- Wasu kuwa sun ce tabbas wannan salon ne sabon gayu, wadanda basu je ko ina a duniyar gayu bane suke sukarsa
Legas - Kashim Shettima, 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya janyo cece-kuce sakamakon shigar da yayi zuwa taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya na wannan shekarar.
A ranar Litinin, tsohon gwamnan jihar Bornon ya wakilci Bola Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a taron NBA da aakayi a Eko Atlantic City daga ranar 22 ga watan Agusta zuwa 26.
Ya bayyana a taron zanzare cikin kwat amma sai ya saka takalman motsa jiki.
Wannan shigar tashi babu shakka ta janyo martani daban-daban a soshiyal midiya ballantana Twitter.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jama'a da yawa sun caccaki salon gayunsa inda suke cewa da bai saka irin takalmin ba a wannan taron.
A yayin shiga tattaunawar, Reno Omokri, tsohon hadimin Goodluck Jonathan, ya yi mamakin yadda 'dan siyasan ke fatan magance matsalolin kasar nan idan an zabe shi duk da bai iya saka kaya yadda ya dace ba.
"Wannan ne abokin tafiyar Tinubu a taron NBA a yau. Duba kafafunsa. Waye cikin hankalinsa zai saka irin kayan nan sannan ya saka takalmin nan kamar zai je motsa jiki?" ya rubuta.
"Idan Shettima bai iya saka kaya ba, ta yaya yake tunanin zai iya shawo kan kalubalen kasar nan?" wani ya tambaya.
“Manta da rigar shi dake kama da wacce kafinta yayi da kuma gamin gambizan takalminsa. Amma ubangidansa na batun dannen fushi ko? Kullum Shettima ransa a bace yake," wani ya rubuta.
Wasu kadan sun kare shi
"Abun takaici ne yadda 'yan Najeriya ke zunden Shettima kan saka kwat da takalmin wasa. Ashe ba su san ma wacce duniyar gayu ake yanzu ba," wani ya rubuta.
"Yauwa Shettima, koyawa jahilan makiyan yadda ake gayun zamani," wani yace.
Babu Gwamnatin Da Ta Kai Buhari Kokari a Bangaren Gine-Gine a Tarihin Najeriya, Lai Mohammed
A wani labari na daban, ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa ginin sabon tashar jirgin saman kasa da kasa ta Murtala Mohammed dake Legas, wani karn hujja ne dake nuna jajircewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Lai Mohammed ya bayyana hakan ranar Litnin yayin yawon ganin idon da ya kai wajen, ma'aikatar Labarai ta bayyana hakan.
A cewarsa:
"Wannan gini - da wasu ire-irensa - hujja ne dake nuna jajircewar gwamnatin Buhari wajen gine-gine irinsu tituna, gadoji, layin dogo, tashoshin ruwa, dss."
Asali: Legit.ng