An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe
- Yan sanda a Jihar Yobe sun yi nasarar kama wasu sojoji guda biyu da ake zargi da hannu wurin kashe Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe tare da sace motarsa
- Sojojin da aka kama sune Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Adamu Gideon na 241 Recce Battalion, Nguru, Jihar Yobe
- Dungus Abdulkarim, mai magana da yawun rundunar yan sandan Yobe ya tabbatar da kama sojojin biyu ya kuma ce an kai su SCID a Damaturu domin zurfafa bincike
Yobe - Rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.
Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin sun ce an bindige shi ne har lahira yayin da sojojin suka tafi da motarsa, jar Honda Accord (Discussion Continues) kafin yan sanda suka kama su, Daily Nigerian ta rahoto.
Yan sanda sun bayyana sunayen wadanda ake zargin
Kakakin yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma ce sojojin biyu da aka kama sune, Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Adamu Gideon na 241 Recce Battalion, Nguru, Jihar Yobe.
Ya ce an kai wadanda ake zargin biyu sashin binciken manyan laifuka na SCID da ke Damaturu don zurfafa bincike, rahoton Leadership.
An birne shahararren malamin a ranar Asabar a garin Gashua ta Jihar Yobe yayin da dubban yan uwa, dalibai da abokansa ke zubar da hawaye.
Yan bindiga sun kashe Shehin Malami, Goni Asami, a jihar Yobe
Tunda farko, rahoto ya zo cewa wasu yan bindiga a ranar Asabar sun hallaka wani Shehin Malami mazauni jihar Yobe, Sheikh Goni Aisamu-Gashua a Jajimaji, hedkwatar karamar hukumar Karasua ta jihar.
Rahoto ya nuna cewa Malamin na hanyarsa ta zuwa Gashua ne daga jihar Kano yayinda suka biyoshi a baya kuma suka bindigesa.
Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 10 na safe a Jajimaji, mai nisan kilomita 10 da Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawan Najeriya.
Asali: Legit.ng