Sojojin Najeriya Sama Da 240 Sun Nemi Fita Daga Aikin Soja

Sojojin Najeriya Sama Da 240 Sun Nemi Fita Daga Aikin Soja

  • Wasu jami'an Sojojin kasan Najeriya sun gabatar da bukatar ritaya daga aikin Soja gaba daya
  • Kakakin hukumar Sojin ya ce aikin Soja ba dole bane kuma kwanan nan sun dauki sabbin Sojoji 5000
  • Jaruman Sojin Najeriya sun fara samun galaba kan yan bindiga a dazukan Arewa maso yamma

Abuja - Hukumar Sojin Najeriya ta amince da bukatar ajiye aiki da wasu Sojoji 243 sukayi saboda wasu dalilai na kansu da kuma na lafiya.

Hukumar ta bukaci su gabatar da kansu ofishin tattara bayanan soji ranar 15 ga Oktoba, 2022, bisa takardar rahoto da Leadership ta gano.

An amince Sojojin suyi ritaya fari da ranar 15 ga Junairun 2023.

A takardar mai lamba AHQ DOAA/G/300//92 mai taken, "Amincewa da ritayar Sojoji bisa bukatar da sukayi na ganin dama da kuma rashin lafiya 2022 91NA/32/4792 WO Ndagana Ishiaku -clk SD A1 da wasu mutum 242" an bukaci Sojin su ajiye dukkan dukiyar gwamnati dake hannunsu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun sako wata tsohuwa mai shekaru 90 da aka sace a jirgin Kaduna

Wani sashen takardar yace:

"An umurceni in bukaci ku sanar da sassan da wadannan Soji suke a saki Sojojin su garzaya Hedkwata da takardunsu ranar 15 ga Oktoba 2022 da hotunansu kuma a tabbatar da cewa dukkan dukiyar Soji dake hannunsu, bindigogi da kayan sarki an kwace."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar Soji
Sojojin Najeriya Sama Da 240 Sun Nemi Fita Daga Aikin Soja
Asali: Facebook

Diraktan hulda da jama'a na hukumar Soja, Birgediya Janar Onyeam Nwachukwu, ya tabbatar da wannan labari, inji Leadership.

Yace aikin Soja ba dole bane kuma kwanan nan sun dauki sabbin Sojoji 5000.

A jawabinsa:

"Sojojin sun nema a sakesu kuma shugaba ya amince, wasu sun nema ne don lafiyarsu saboda basu da karfin cigaba da aikin."
"Idan mutum yace ba zai iya cigaba da abu ba, shin za ka tilasta masa ne? Sauran kuma sunce sun gaji zasu ajiye aikin. Hukumar Soji ba dole bace. Kwanan nan muka dauki mutum 5000."

Kara karanta wannan

Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta

Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Rikakken 'Dan Bindiga Lawal Kwalba, Sun Kwato Kayan Hada Bama-bamai

A wani labarin kuwa, Jami'an tsaro a jihar Kaduna a ranar Alhamis sun kai samame maboyar rikakken 'dan bindiga Lawan Kwalba a karamar hukumar Chikun ta jihar inda suka samo kayayyakin hada bama-bamai.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, yace jami'an tsaron sun samo buhunan taki 27 wadanda ake amfani da su wurin hada abubuwa masu fashewa a cikin dajin Chikun

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida