Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya

Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya

  • Har Ila Yau, ana cigaba da zaman doya da manja tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike
  • Kwamitin Sulhun da aka nada ta sake zama ranar Juma'a amma abin ya ki daidaituwa
  • Gwamna Wike ya shiga adawa da Atiku ne bisa rashin zabensa matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fatakwal - Mambobin kwamitin sulhu tsakanin dan takarar kujeran shugaban kasar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar da Gwamnan jihar RIvers, Nyesom Wike, sun sake zama.

Mambobin sun tattauna na tsawon sa'o'i hudu a birnin Fatakwal ranar Juma'a, 19 ga watan Agusta amma har yanzu abin ya ci tura, rahoton ThisDay.

Wike na cigaba da nuna adawarsa ga Atiku Abubakar bisa rashin zabensa matsayin abokin tafiya a tikitin takara.

Atiku Wike
Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya Hoto: Atiku/Wike
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sashen Atiku da na Wike sun shiga ganawar sirri sasanta jiga-jigan biyu

Wanda ya jagoranci kwamitin sulhun kuma tsohon Gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, bayan zaman a bayyana cewa har yanzu da sauran rina a kaba kuma zasu yi sabon zama.

A cewarsa:

"Wannan sulhu ne, akwai wasu abubuwan dake bukata tattaunawa mai zurfi idan kwamitin ya sake zama."

Majiyoyi sun bayyana cewa babban matsalar da ake fama da ita yanzu itace kafewar Wike kan cewa lallai sai an tsige Shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, riwayar AriseNews.

Wadanda suka wakilci Atiku a zaman sun hada da Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, Hon Adamu Waziri da kuma Eyitayo Jegede.

Wakilan Wike kuwa sun hada da tsohon Ministan Shari'a, Bello Adoke; Gwamnan Okezie Ikpeazu na Abi; Tsohon gwamnan Rivers, Donald Duke da tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Damkwambo.

Wakilin Atiku, Gwamna Fintiri, ya laburtawa manema labarai cewa suna kyautata zaton za'a samar da zamar lafiya mai wanzuwa cikin jam'iyyar ta adawa.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu

Yace:

"Komin daren dadewa zamuyi sulhu kuma zamu hada kan yan jam'iyya da yan Najeriya."

Daga baya mambobin kwamitin suka gana da Wike a gidansa dake Rumueprikom, karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

"Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi

Daya cikin wadanda aka kafa jam'iyyar PDP da su kuma mamba na kwamitin amintattu, Cif Bode George, ya ce rikicin cikin gidan na jam'iyyar na damunsa, yana mai cewa shedan ya ratsa jam'iyyar, Daily Trust ta rahoto.

Jiga-jigan jam'iyyar na PDP da dama sun bada shawarar Wike ya zama mataimakin Atiku amma tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi gwamnan Jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa. Rikicin jam'iyyar ya kara rincabewa bayan hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida