Mutum Bakwai Yan Gida Daya Sun Rasu Bayan Cin Dambu Mai Guba a Jihar Zamfara
- Baki ɗaya iyali mai mutum Bakwai sun rasu bayan cin 'Dambu' a ƙauyen Danbaza, ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara
- Kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce tuni suka fara bincike kan lamarin kuma sun ɗebo abincin da mamatan suka ci
- Wani makusancin iyalan ya ce nan take mutum hudu suka rasu bayan gama cin abincin, sauran kuma sai da aka je asibiti
Zamfara - Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ta ce wasu mutum Bakwai ƴan gida ɗaya sun rasa rayukansu bayan sun ci abincin gargajiya 'Dambu' lokacin cin abincin dare, Vanguard ta ruwaito.
Mai magana yawun hukumar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, shi ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
Shehu ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin rasuwar iyalan ƴan gida ɗaya a ƙauyen Dambaza da ke ƙaramar hukumar Maradun, a jihar Zamfara.
Daily Nigerian ta rahoto a jawabinsa SP Shehu ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lamarin ya auku ranar Litinin jim kaɗan bayan iyalan sun kammala cin abincin da aka shirya musu na dare."
"Hukumar yan sanda ta ɗibo irin abincin da suka ci domin gudanar da bincike kuma ina tabbatar wa al'umma cewa za mu fallasa sakamakon abinda muka gano ga manema labarai."
Yadda lamarin ya faru
Wani mazaunin ƙauyen, Muhammad Kabir, wanda ke da kusanci da iyalan, ya shaida wa NAN cewa hudu daga cikin iyalan da suka haɗa da matan aure biyu da yara sun rasu nan take, yayin da ragowar mutum uku suka ce ga garin ku nan bayan kai su Asibiti mafi kusa.
Har Yanzun Akwai Sauran Fasinjojin Jirgin Ƙasa a Hannun Yan Ta'adda, Mamu Ya Faɗi Mummunan Halin Da Suke Ciki
"Iyalan na kammala cin abincin da aka shirya musu, mutum huɗu suka rasu nan take a wurin, sauran mutum uku kuma sai da aka gaggauta kai su Asibiti, amma daga baya suka ce ga garin ku nan ana cikin ba su kulawa."
A wani labarin kuma Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Saduwa Da Ni, Matar Aure ta fada wa Kotu
Wata Mata da ke neman a raba aurenta ta faɗa wa Kotu makasudin da yasa wasu lokutan take hana mijinta kwanciya da ita.
Matar ta kai karar mijin gaban Kotun kostumare da ke Ibadan, jihar Oyo ne saboda tace tana rayuwar baƙin ciki da 'ya'yanta.
Asali: Legit.ng