Bidiyo: Kyakyawar Baturiya na Neman Kudi a Kasuwa, Tana Nika da Siyar da Garin Tuwo

Bidiyo: Kyakyawar Baturiya na Neman Kudi a Kasuwa, Tana Nika da Siyar da Garin Tuwo

  • Wata kyakyawar budurwa baturiya ta bayyana cikin cunkoson kasuwar Najeriya tana taimakawa mata 'yan kasuwa siyar da hajojinsu
  • A bidiyon, an ganta tana taimakawa wurin markada kayan miya, siyar da garin tuwo ga kwastomomi yayin da ta daura zani cike da alfahari
  • Matashiyar budurwar ta bayyana bidiyon a YouTube da TikTok kuma tace ta ji dadin lokacin da ta kwashe tana ayyuka a cikin kasuwar

Wata budurwar baturiya ta yanke hukuncin jin yadda kasuwar Najeriya take, hakan yasa ta shiga daya daga ciki inda ta taimakawa mata 'yan kasuwa yin harkokin kasuwanci masu yawa.

A bidiyon da ta saka a TikTok da YouTube, tace ta je kasuwar ne neman kudi wanda hakan ake cewa a matsayin aiki tukuru a Najeriya.

Baturiya mai nema
Bidiyo: Kyakyawar Baturiya na Neman Kudi a Kasuwa, Tana Nika da Siyar da Garin Tuwo. Hoto daga TikTok/@pia.majiq
Asali: UGC

Wannan abun yayi min dadi

A bidiyon da ta fitar, an ganta sanye da riga irin ta kuku wacce mata 'yan kasuwa ke sanyawa kuma tana taimakawa wurin siyar da abinci.

Kara karanta wannan

Babu haske: An kammala ganawar gwamnatin Buhari da ASUU, sakamako bai yi dadi ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da take kasuwar, ta kara da taimako wurin yin markade, lamarin da ya birge jama'a da yawa da suka ga bidiyon.

Kyakyawar budurwar an gano sunanta da Pia Majiq a TikTok, tace a gaskiya ta ji dadin irin gogewar da ta samu na taimakon mata kasuwar.

Kalla bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a TikTok

A yayin da jama'a suka ci karo da bidiyon, sun dinga yabawa kan kokarinta a cikin kasuwar. Ga wasu daga cikin tsokacin:

@Bash:

"Da gaske kike? Ba taba tsammanin zaki iya yin duka ayyukan nan na."

@Isa:

"Kai, wannan abu ya birge."

@kaylah:

"Muna miki maraba, muna kaunarki tuntuni."

@swt302:

"Wannan yasa na kara son ki sosai."

Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya

A wani labari na daban, Usman Ekukoyi, wani 'dan Najeriya dake siyar da gwanjo ya bayyana labarin yadda rayuwarsa ta sauya gaba daya.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

A bidiyon da ya fitar a TikTok, Usman ya bayyana yadda ya fara kasuwancinsa da jari kalilan amma Ubangiji ya taimaka masa yanzu ya shahara.

A shekarun da suka gabata, Usman ya saba siyar da kaya a gefen titin jami'ar fasaha tarayya dake Akure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng