Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya
- Wani mutum 'dan Najeriya mai suna Usman Ekukoyi ya bayyana bidiyon katafaren shagon siyar da sutturu da yake siyarwa
- A yayin bayyana bidiyon a TikTok, ya sanar da yadda ya fara da tallar gwanjo, siyar da shi a gefen titi da irin fadi tashin da yayi
- Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun jinjina masa kan yadda ya dage ya nemi na kansa har ya tsayu da kafafunsa a garin kamar Legas
Legas - Usman Ekukoyi, wani 'dan Najeriya dake siyar da gwanjo ya bayyana labarin yadda rayuwarsa ta sauya gaba daya.
A bidiyon da ya fitar a TikTok, Usman ya bayyana yadda ya fara kasuwancinsa da jari kalilan amma Ubangiji ya taimaka masa yanzu ya shahara.
A shekarun da suka gabata, Usman ya saba siyar da kaya a gefen titin jami'ar fasaha tarayya dake Akure.
A wasu lokaci, ya kan tattaka yayi talla a cikin jami'a ko kuma ya kai har dakunan kwanan dalibai inda daliban ke tururuwar siyan kayan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Na fara daga ba komai, daga tushe. Ranakun da nake tsallake ajujuwa, gwaji, in tafi har Legas daga FUTA don saro gwanjo kuma in siyar a makaranta.
"A ranakun tattaki da talla daga dakunan kwanan dalibai daban-daban. Ubangiji ya daukaka. Wannan yaron ya zama mai manyan shaguna biyu a tsibirin Mandilas dake Legas."
Kalla bidiyon:
Jama'a sun yi martani
Moponz tace:
"Ya aka yi ka samu kudi har ka gina wannan katafaren shagon, bamu labari."
Hairybeautybar_ tace:
"Hakuri da jajircewa."
Kwamezack_:
"Wannan karin karfin guiwa ne."
Officialbidun:
"Ubangiji yayi mana albarka baki daya."
Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai
A wani labari na daban, wani karamin yaro daga karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa ya birge ma'abota amfani da soshiyal midiya bayan yayi shiga sak ta Tinubu.
Yaron da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya yadu a gajeren bidiyon inda yake sanye da lankwasassar hular Yarabawa wacce Tinubu ya saba sanyawa.
An gan shi a bidiyon sanye irin gilashin da jigon APC din yake sanyawa na tsawon shekaru.
Ba wai shi kadai ba, yaron ya cigaba da yawo a cikin tawaga da magoya baya kamar yadda aka kuma ganinsa yana jawabi ga taron jama'a a abinda yayi kama da wurin kamfen.
Asali: Legit.ng