Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hawa Babura, Ta Ce Duk Wanda Aka Gani a Kai a Harbe
- Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana haramta hawa babura a wasu yankunan jihar saboda barkewar lamarin tsaro
- A baya gwamnatin jihar ta bayyana sabuwar doka ta hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da aikata bindiganci
- Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na daga yankunan kasar da ke fama da matsalar rashin tsaro matsananci
Gusau, jihar Zamfara - Duba da sake tabarbarewar tsaro a Zamfara, Gwamna Bello Mattawale a ranar Litinin ya haramta hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a garin Gusau.
Ya umurci jami’an tsaro da su harbe duk wanda aka samu ya saba wannan sabon dokar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewar gwamnan, an dauki matakin ne biyo bayan rahotannin yadda ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ke amfani da babura wajen aikata muggan laifuka a cikin babban birnin jihar da kewayenta.
Da yake bayyana yankunan da lamarin ya shafa, matawalle ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wadannan yankuna sun hada da Mareri, Damba, Tsunami, Tsauni, Barakallahu, Samaru, Gada Biyu, da Janyau Gabas”.
“An umurci jami’an tsaro da su bindige duk wanda ya hau babur tsakanin karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a wajen garin Gusau, wanda ya ki tsayawa idan aka umarce shi da ya yi hakan.
“A halin da ake ciki, an yi kira ga jama’a da su sanya ido a yankunansu tare da kai rahoto ga jami’an tsaro na duk wani mutum da ake zargi ko wani bakon motsi a yankunan.”
"Gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da duk wanda aka samu yana kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jama'a ba".
Gwamnan ya jaddada cewa, tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa shi ne babban aikin kowace gwamnati, kamar yadda SolaceBase ta kawo.
Ya kara da cewa:
"Gwamnatina tana yin duk mai yiwuwa bisa ga dokokin kasa don tabbatar da sauke wannan nauyi."
Yan Bindiga da Masu Kai Musu Bayanai Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa, Inji Matawalle Na Zamfara
A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, tsafi, ko kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.
Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani sako da ya sanarwa al’ummar jihar a safiyar ranar Talata 16 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.
Matawalle ya ce: “A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, tsafi, garkuwa da mutane da sauran laifukan da sukashafe su, 2022.
Asali: Legit.ng