Bidiyoyi da Hotuna: Dirarriyar Amarya ta yi Shiga Kala 10 Masu Kayatarwa a Ranar Aurenta

Bidiyoyi da Hotuna: Dirarriyar Amarya ta yi Shiga Kala 10 Masu Kayatarwa a Ranar Aurenta

  • Wata amarya 'yar Afrika mai suna Zainab Ibrahim, ta tada kura a soshiyal midiya a ranar aurenta da irin shigar amaren zamani da ta dinga yi
  • Kyakyawa kuma dirarriyar amaryar ta zama abun magana bayan ta saka kaya kala goma masu tsada a ranar aurenta da masoyinta kuma angonta
  • Hotuna da bidiyoyin amarya sun yadu a kafafen sada zumuntar zamani yayin da masoyanta suka dinga yaba tsarin surarta da salonta

Wata amarya 'yar Afrika mai suna Zainab Ibrahim ta kafa wani babban tarihi a ranar aurenta inda ta saka kaya tsadaddu har kala goma.

Shagalin aure a Afrika yana kasancewa babban lamari kuma salon da jama'a da yawa ke bi wurin nuna isarsu da arzikinsu ta hanyar daka sutturu masu tsada.

Dirarriyar Amarya
Bidiyoyi da Hotuna: Dirarriyar Amarya ta yi Shiga Kala 10 Masu Kayatarwa a Ranar Auren. Hoto daga @asoebiafrica
Asali: Instagram

A cikin kwanakin nan ne Zainab Ibrahim ta zama abun magana da kwatance bayan bidiyoyi da hotunan aurenta sun lkarade soshiyal midiya sakamakon kaya kala goma da ta dinga sanyawa tana cire a ranar aurenta.

Kara karanta wannan

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakkyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yawa daga cikin shigar da Zainab tayi, kayan an yi su ne da tsadaddun yadika kuma aka yti musu dinkunan kece raini.

Ba a nan amarya Zainab Ibrahim ta tsaya ba, ta kawata kwalliyarta da tsadaddun sarkoki da 'ytan kunnaye yayin da kalolin klayan da ta saka kadai suka zama abun kallo.

Wasu daga cikin launikan sutturun da amaryar ta saka sun hada da fari, ja, kalar hantar kare, ruwan ganye, kalar sararin samaniya da sauransu.

Ma'abota amfani da intanet sun dinga yaba shiga 10 ta Zainab a ranar aurenta

Amaryar Afrikan ta gigita jama'a da hotunanta tare da bidiyoyin irin shigarta wanda hakan yasa 'yan soshiyal midiya suka dinga tsokaci tare da yabawa.

Karanta wasu daga cikin tsokacinsu.

Dpotterscatering:

“A gaskiya tayi matukar kyau a dukkan shigarta, ina taya ki murna."

Kara karanta wannan

Fulani ga Miyetti Allah: Yanzu dai mun waye, za mu zabi cancanta ne ba addini ko kabila ba

Nettebeeofficial:

“'Yar juwa gaskiya kin matukar tasarmu."

Ibinike_:

“Kwarin guiwarta shi ke walwali daga cikin kowanne kaya da ta saka."

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

A wani labari na daban, bidiyon wata doguwar amarya tare da guntun angonta ya janyo cece-kuce mai yawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Bidiyon ya nuna lokacin da angon gajere ya shiga wurin liyafar tare da amaryarsa, wacce ko kusa ba tsawonsu daya ba.

A gajeren bidiyon da aka gani a Instagram, an ga angon yana ta tikar rawa shi kadai a wurin liyafar yayin da matarsa take zaune kuma tana magana da wani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng