Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai
- Wani yaro karami 'dan Najeriya daga karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa ya yadu bayan yin shiga sak irin ta Tinubu
- A gajeren bidiyon dake nuna yaron sanye da hular Yarabawa lankwasassa irin ta 'dan takarar APC, ya fito sak kamar tsara shi aka yi
- Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun bayyana cewa, yaron ya birgesu yayin da magoya bayan Tinubu suka ce bidiyon na nuna tsabar sunan da Tinubu yayi a arewa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Mayo Belwa, Adamawa - Wani karamin yaro daga karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa ya birge ma'abota amfani da soshiyal midiya bayan yayi shiga sak ta Tinubu.
Yaron da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya yadu a gajeren bidiyon inda yake sanye da lankwasassar hular Yarabawa wacce Tinubu ya saba sanyawa.
Tinubu zai zama shugaban kasa, Masoyansa suka ce
An gan shi a bidiyon sanye irin gilashin da jigon APC din yake sanyawa na tsawon shekaru.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba wai shi kadai ba, yaron ya cigaba da yawo a cikin tawaga da magoya baya kamar yadda aka kuma ganinsa yana jawabi ga taron jama'a a abinda yayi kama da wurin kamfen.
jama'a masu tarin yawa sun kalla bidiyon a Facebook yayin da wasu magoya bayan Tinubu suke ta murna kan ganin irin wannan abu ya faru da 'dan takararsu.
Jama'a sun yi martani
Oluwaseun Adeniyi yace:
"Jagaban shine zai zama Shugaban kasa na nan gaba, da sunan Yesu Almasihu..."
Ismail Adepeju yace:
"Godiya muke da kayi wannan abu, Asiwaju Bola Tinubu shine shugaban kasan mu a gaba da izinin Ubangiji."
Orudunsu Sunday yace:
"Karamin Tinubu, zaka zama babban mutum da sunan Yesu Almasihu. 'Yan arewa sune kwararru a harkar."
Badejo Adebowale Solomon yace:
"Zan so Tinubu yayi kamar yadda yayi yana gwamna. Ya zama shugaban kasa ga matasa idan ya zama shugaban kasa."
Charles Leedee yace:
"Ko ana so, ko ba a so, Bola Tinubu zai zama shugabannin kasan Najeriya nan da 2023 da izinin Ubangiji."
Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi
A wani labari na daban, Yemi Farounbi, tsohon ambasadan Najeriya a kasar Philippine, yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ladabtarwar ce daga Ubangiji da ake yi wa 'yan Najeriya.
The Cable ta ruwaito cewa, Farounbi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da aka tattauna da shi a shirin gidan rediyo a Ayekooto a Splash 105.5FM.
Yace an ja kunnen 'yan Najeriya kan tarihin Buhari da kuma yadda ya garkame 'yan siyasa masu tarin yawa.
Asali: Legit.ng