'Yan Najeriya Za Su Shiga Duhu, Ma’aikatan Lantarki Za Su Shiga Yajin Aiki
Alamu na nuna cewa matsalar wutar lantarki a Najeriya na iya kara kamari daga ranar Laraba, yayin da kungiyar kwadago ta umarci ma’aikata a bangaren wutar lantarki su shiga yajin aikin sai baba ta gani.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yajin aikin na ma'aikatan wutar lantarki na nasaba da matsaloli tsakanin ma'aikatan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), Vanguard ta ruwaito.
A karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), a matsayin share fage na yajin aikin, ma’aikatan na shirin mamaye babban ofishin TCN na kasa da ke Abuja a ranar Talata.
A wata wasika da Babban Sakataren NUEE, Joe Ajaero ya fitar ta umarci manyan mataimakan sakatarori na kungiyar da su tabbatar da cikakken bin hadin kai ga yajin.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng