Ka Kammala Aikin Titi cikin wata 4, Gwamnati Ta Ba yiwa Dan Kwangila Gargadi

Ka Kammala Aikin Titi cikin wata 4, Gwamnati Ta Ba yiwa Dan Kwangila Gargadi

  • Gwamnatin tarayya ta ba Dantata & Sawoe dake aikin gina titin Western Bypass da ke birnin jihar Kano wa’adin watannin hudu ta kamala aikin
  • Ministan a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ya ce za a samar da dukkan kudaden da ake bukata dan ganin a kammala duka ayyukan da suka fara kafin gwamnatin su ya kare
  • Kamfanin Dantata & Sawoe ta ce zata gama aikin titin Western Bypass kafin wa'adin da aka bata ta kammala ya kure

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Gwamnatin tarayya ta ba Dantata & Sawoe dake aikin gina titin Western Bypass da ke birnin jihar Kano wa’adin watannin hudu ta kamala aikin. Rahoton Aminiya

Ministan a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub ne ya bayyana haka a ranar Asabar, a lokacin da yaje duba aikin titin mai tsawon kilomita 26 inda ya bada karshen karshen watan Disamban 2022 a kamala aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni: Ma'aikata a jiha ta na morewa, bana fashi ko jinkirin biyan albashi

Umar Ibrahim EL-Yakub ya koka kan yadda ya ce aikin na tafiyar hawainiya, inda ya ce ya zama wajibi kamfanin ya kammala shi nan da karshen shekarar da muke ciki.

Kanon
Gwamnati Ta Ba Dan Kwangila Wata 4 Ya Kammala Aikin Titi A Kano FOTO The Guardian Nigria
Asali: UGC

Umar Ibrahim ya ce za su samar da dukkan kudaden da ake bukata ga aikin don tabbatar da gama ayyukan da suka fara karfin wa’danin gwamnatin Buhari ya kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Injiniyan da ke kula da aikin, Alhaji Kasimu Maigwandu, yayi korafi akan da yadda farashin kayayyaki aiki suka yi tashin gwarzon zabi, musamman man dizel wanda shine babban matsalar su

Alhaji Kasimu ya ce sun kammala kashi 71 daga cikin 100 na aikin, kuma suna suna sa ran za su kammala sauran aikin kafin wa’adin da aka basu ya cika.

Abu Uku Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna - Isa Ashiru

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

A wani labari kuma, Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna Jam'iyyar PDP ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna. Rahoton BBC

Ashiru Kudan wanda ke takarar gwamnan jihar Kaduna karo na uku yace abun na farko da zai fara ba muhimmanci a jihar shine fannin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa