Rashin Zaɓen Shugabanni Nagari a 2023 Zai Rusa Najeriya, Obasanjo
- Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gargaɗi yan Najeriya su yi karatun ta nutsu wajen zaɓen 2023 da ke tafe
- Obasanjo ya ce idan aka yi kuskuren zaɓen shugabanni a zaɓe na gaba, Najeriya ka iya rushe wa
- Tsohon Shugaban ya yi wannan furucin ne a wurin wani taro da ya halarta a matsayin babban bako a jihar Legas
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a ranar Laraba ya roki yan Najeriya su yi karatun ta nutsu su zaɓi shuwagabanni nagari a zaɓen 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obasanjo ya gargaɗi yan Najeriya da cewa zaɓen gurɓatattun shugabannini a zaɓe mai zuwa zai iya rusa ƙasar baki ɗaya.
Tsohon shugaban ya yi wannan furucin ne a matsayinsa na babban bako a wurin taron shekara-shekara na gidauniyar Wilson Badejo karo na 15 wanda ya gudana a Legas.
A wurin taron mai taken, "Shawo kan tagwayen ƙalubale, talauci da matsalar tsaro a Najeriya," Obasanjo ya bayyana yaƙinin cewa idan har aka zaɓi mutane na gari a 2023, to Najeriya zata cigaba sosai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Channels tv ta tattaro a jawabinsa ya ce:
"Ɗayan biyu ne, Ko dai mu zabi shugabanni nagari saboda idan mun ci nasarar zaɓen mutane nagartattu to zamu kai wurin da muke mafarkin kai wa."
"Idan kuma muka yi kuskure muka yi zaɓen tumun dare, to abubuwa zasu rusa mu, muna fatan Allah ya kare mu daga wannan, amma wajibi mu yi zaɓen da ya dace a 2023."
Tun da farko, tsohon shugaban ya ce har yanzun Najeriya ba ta kai inda ya dace a ganta ba saboda talauci da rashin zaman lafiya.
"Najeriya ba ta kai matsayin da ya kamata a ganta ba, duk wanda ya ce komai na tafiya dai-dai, tabbas wannan mutumin na bukatar a masa gwajin kwakwalwa."
Wata Sabuwa: Gwamnan APC Ya Faɗi Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Ɗayansu Ya Gaji Buhari a 2023
Wajibi mulki ya koma kudu a 2023 - Akeredolu
A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Faɗi Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Ɗayansu Ya Gaji Buhari a 2023
Gwamnan Ondo na jam'iyyar APC mai mulki ya ce ko Peter Obi ya lashe zaɓen 2023 a wurinsa babu wani abun damuwa.
Gwamna Rotimi Akeredolu ya jima yana jaddada cewa wajibi mulkin Najeriya ya koma kudanci a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng