Hazikin Yaro da ya Samu A Bakwai da B daya a WASSCE Ya Rasa Gurbin Karatu a Jami'a

Hazikin Yaro da ya Samu A Bakwai da B daya a WASSCE Ya Rasa Gurbin Karatu a Jami'a

  • Francis Assan, hazikin dalibi 'dan kasar Ghana ne da ya samu A bakwai sai B daya a Social Studies bayan ya rubuta jarabawar WASSCE, ya rasa gurbin karatu a jami'ar Ghana
  • Ya yanke shawarar samun digiri a fannin kudi a jami'ar kwararru dake Accra, UPSA inda ya kammala da sakamako mai matukar kyau
  • Matashin ya kammala digirinsa cike da sa'a tare da sakamako mai kyau kuma yana neman aiki da kamfani mai kyau a Ghana

Ghana- Wani matashi ya bayar da labarin yadda 'dan uwan shi ya rasa gurbin karatu a jami'a duk da ya samu A bakwai a jarabawar kammala sakandare ta WASSCE.

An ga wallafar a LinkedIn, shafin Dickson Assan inda yake bayyana cewa jami'ar karatun shari'a ta Ghana ce ta hana matashin gurbin karatu saboda ya samu B a darasin Social Studies duk da A bakwai da ya samu a dukkan darussan da ya rubuta.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Najeriya Ya Badda Kamanni A Matsayin Mace A Facebook, Ya Damfari Dan Indiya Naira Miliyan 31

WASSCE
Hazikin Yaro da ya Samu A Bakwai da B daya a WASSCE Ya Rasa Gurbin Karatu a Jami'a. Hoto daga Dickson Assan/LinkedIn
Asali: UGC

Ya rubuta: "

A dalilin da yasa jami'ar Ghana ta hana kanina Francis gurbin karatun shari'a, har yanzu ina mamaki. A garesu samun B2 a Social Studies ba hazaka bace."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Dickson yace, dan uwansa bashi da wani zabi da ya wuce ya nemi wata jami'ar tunda jami'ar Ghana sun hana shi gurbin karatu.

Cike da sa'a, ya samu gurbin karatu a jami'ar karatuttukan kwararru dake Accra, UPSA, inda ya karanci Accounting and Finance kuma ya kammala digirinsa.

A matsayinsa na hazikin mutum, Francis ya kammala digirinsa da sakamako mai matukar kyau.

Babban yayanshi ya bayyana jin dadinsa kuma ya dinga yabawa kaninsa ta yadda yasa dangi ake alfahari da shi duk da abinda ya fuskanta na koma baya a baya.

Francis Abban a halin yanzu yana jiran aikin yi tare da fatan samun mai nagarta.

Kara karanta wannan

Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro

Da Kaina Zan Zaba Miji In Darje: Budurwa Dake Sana'ar Hakar Burtsatsai

A wani labari na daban, wata budurwa 'yan Najeriya mai suna Maryam Hussain, wacce ke haka burtsatsai a matsayin sana'a ta shawarci matasa da masu digiri da su kirkiri sana'a a maimakon jiran aikin gwamnati.

A tattaunawarta da BBC News Pidgin, zakakurar budurwar ta bayyana yadda ta fada aikin da aka san maza da shi. Maryam tace mutane na zundenta a lokacin da ta fara wannan sana'ar.

Maryam wacce ke da digiri a fannin fasahar katako, tace tuntuni ta so bude shagonta na kanta.

Amma saboda rashin kudi da kuma irin gidan da ta fito, bata samu kudin yin hakan ba wanda yasa ta koma haka burtsatsai. Maryam tace ta kwashe sama da shekaru 10 tana haka burtsatsai a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng