Caca : Wani Matashi Ya Fashe Da Kuka Bayan Yayi Asarar Naira 11,800 kudin aike
- Wani Matashi a kasar Ghana ya fashe da kuka bayan yayi asarar GH¢250 (N11, 800) da maigidan sa ya ba shi siyo kayayyakin gini a wajen caca
- Wanda ya bada labarin Lamarin A cikin wani faifan bidiyo, ya bayyana cewa matashin ya caca da GH¢250 (N11,800) da nufin ninka kudin
- Wani da yayi sharhi a soshiyal midiya ya ce kwadayi mabudi wahala, kwadayi na iya saka mutum cikin wahalar da bai shirya shiga ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ghana - Wani matashi a Ghana ya fashe da kuka yayin da ya yi asarar GH¢250 (N11, 800) da maigidan sa ya ba shi siyo kayayyakin gini a wajen cacar wasanni. Rahoton Yen.com
A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda Legit.ng ta gani, wani mai ba da labari ya bayyana cewa maigidansa ne ya aike shi ya siyo kayan gini da kudin.
Yayin da yake daukar bidiyon lamarin a waya, mai ba da labarin ya tambayi matashin ko yana budurwa da yan uwa da zasu taimake shi.
Joel Eshun, ya yada bidiyon ne a shafin a tuwita mai sunna @JOELESHUN4, wanda ya janyo martani daga wurin mutane da dama .
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga Irin martani da Mutane Suka yi Game da Bidiyon
@orlando_osman ya ce, Ah a za’ayi mutum ya kashe, Ghc250 (N11, 800) a caca watakila shi mafari ne
@asumadulive yayi sharhi da cewa daga karshe ya shiga taitayin sa! Nana Kafra.
@RthurMichael yayi sharhi da cewa kwadayi mabudin wahala zai saka ka cikin wahalar da baka shirya shiga ba.
@nosa138318 ya ce gargadi kada kuskura kayi caca akan Manchester United ga yanzu ya kashe kudin aka bashi ya siyo kayan gini
Zaben 2023: Sarkin Musulmi Da CAN Sun Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya
A wani labari kuma, Washington - Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Sa’ad Abubakar III da da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zabe mai zuwa a 2023. Rahoton VANGUARD
Sun kula yarjejeniyar ne a birnin Washington na kasar Amurka dan kawar da duk fitinar da zata taso da fuskan addinin a lokacin gudanar da zabe.
Asali: Legit.ng