Jami’an Hisba Sun Kai samame Wata Makarantar Sakandare a jihar Kano
- Jami’an hukumar Hisba sun kai samame wata Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin Doka a Jihar Kano
- Hisba Ta yiwa wasu dalibai da suka kama da askin banza da kammala karatun sakandare sabuwar askin da ya dace dasu
- Hukumar Hisba a Kano sune dakaru na Addinin Musulunci da alhakin tilastawa al’ummar musulmi yin aiki da shari'ar musulunci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kano - Jami’an hukumar Hisba sun kai samame wata Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin Doka a Jihar Kano.
Jami’an Hisba su kama wasu dalibai da suka yi askin banza don murnar kammala karatun sakandare inda suka musu askin da ya dace da su.
Hukumar Hisbah a Jihar Kano sune dakaru na Addinin Musulunci da alhakin tilastawa al’ummar musulmi yin aiki da shari'ar musulunci.
A hotunan da Daily Nigerian ta wallafa, an ga jami'an hukumar Hisbah sun aske kan wasu matasa da suka canza kalar gashinsu da wadanda suka mayar da nasu irin na mata.
Kalli hotunan:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hisba tana matukar kokarin waje hukunta masu saba ka’aodijin addinin musulunci a jihar kano musaaman wajen kama motoci dake shigowa da kayan barasa jihar da kuma kai kama masu shigar banza.
A baya Legit.NG ta rawaito Labarin yadda hukumar Hisba ta yiwa wani jami’in ta kyautar Naira miliyan daya bayan ya ki karban kudin cin hancin da aka bashi bayan ya kama motar indomie cike da giya.
A lokacin watan Ramadana Hukumar Hisba ta kan kama mutanen dake cin abin cikin a bainar jama’a kuma ta hukunta su.
Duk da kokarin da hukumar Hisba keyi wajen tabatar da duka da oda Wasu mutane na sukan da korafi cewa dokar Hisba bata aikin akan masu kudi sai dai akan talakawa.
Asali: Legit.ng