Gwamnatin Adamawa Ta Maida Ma'aikata 1,699 da Aka Kora Bakin Aiki
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya maida ma'aikata 1,699 bakin aiki bayan gwamnatin baya ta sallame su
- Babban mai taimakawa gwamnan ta fannin yaɗa labarai, Solomon Kumangar, ya ce gwamnatin ta kuma ɗauki sabbin ma'aikata sama da 2,000
- Gwamnatin ta ce bayan gudanar da bincike mai zurfi ta gano cewa an sallami ma'aikatan ne saboda wani kuskure yayin daukar su
Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa karkaashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri, ta maida ma'aikata 1,699 waɗan da gwamnatin baya ta kora, bakin aikinnsu.
Kakakin gwamnan Adamawa, Solomon Kumangar, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin a Yola, babbar birnin jihar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Mista Kumangar ya yi bayanin cewa Malaman Makarantun Firamare da Sakandire 699 na rukunin D waɗan da a baya gwamnati ta sallame su, yanzu an maida su bakin aiki.
Ya kuma ƙara da cewa ƙarin Ma'aikatan lafiya 1,000 zasu koma su cigaba da aikin su saboda gwamnatin baya ta kore su ne saboda karya doka a matakan ɗaukar su aiki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Solomon Kumangar ya ce:
"Mun gudanar da bincike mai zurfi don gano inda aka yi kuskure da nufin gyara wurin da aka ɓata lokacin ɗaukar su aiki domin ba mu son cutar da kowane mutum."
Gwamnatin Fintiri ta ɗauki sabbin ma'aikata
Mai magana da yawun gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin Fintiri ta sake ɗaukar ƙarin Malaman Makarantun Sakandire 2,000 a faɗim sassan jihar Adamawa.
Bugu da ƙari gwamnatin ba ta tsaya iya nan ba, ta ɗauki karin jami'an duba gari (VSO) mutum 70, a cewar Mista Kumangar, kamar yadda PM News ta rahoto
A wani labarin kuma Atiku ya shirya babban gangami, zai tarbi jiga-Jigai da mambobin APC 1,615 da suka koma PDP
Wata Sabuwa a PDP: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fallasa Jiga-Jigan da Suka Haddasa Rikicin Atiku da Wike
Mambobin jam'iyyar APC sama da dubu ɗaya sun sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Adamawa.
A cewar wakilan masu sauya sheƙan ba su kenan ba, sun kai mutum 6,000 da suka yanke barin APC saboda gazawar Buhari.
Asali: Legit.ng