Bidiyo: An Zube Mahajjatan Kano da Suka Dawo Daga Saudi a Abuja Kan Rashin Man Jirgi
- An zube mahajjatan jihar Kano da suka dira Abuja daga kasa mai tsarki a filin jiragin sama na Abuja
- Mahajjatan suna zaune inda suke jiran tsammanin lokacin da za a kai su gida Kano, amma har yanzu shiru
- Hakan ya faru ne sakamakon rashin man da za a sanyawa jirgin sama ya lula da su zuwa jihar Kano daga Abuja
Abuja - An zube mahajjatan Kano da suka dawo daga kasa mai tsarki a filin sauka da tashin jiragen sama dake Abuja kan rashin man jirgin sama da za a karasa da su jiharsu.
Kamar yadda bidiyon da jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter ya bayyana, an ga mahajjatan rashe-rashe a filin jirgin dake Abuja.
Wasu daga cikinsu suna zazzaune a kasa yayin da wasu ke rike da jakunkunansu sun jiran tsammanin lokacin da za a kwashe su zuwa gida domin saduwa sa iyalansu.
NAHCON Ta Kammala Kwaso Alhazan Najeriya Daga Ƙasa Mai Tsarki, Ta Yi Magana Kan Matsalolin Da Aka Samu
Hukumar NAHCON Ta Kammala Kwaso Alhazan Najeriya Daga Saudiyya
A wani labari na daban, hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON ta kammala aikin Hajjin bana 2022 bayan jirgin da ya ɗakko sawun ƙarshe na Alhazan Najeriya ya tashi daga filin jirgin saman Sarki Abdul'Azizi da ke Jiddah da misalin karfe 12:00 na dare.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Jirgin mallakin Kamfanin jiragen sama na Azman Air ya ɗakko Alhazai Najeriya 319 daga ƙasar Saudiyya.
Alhazan da suka kasance a sawun ƙarshen sun ƙunshi mahajjatan jihar Kaduna, jihar Kano, da kuma jami'ai daga jihohi da kuma ma'aikatan hukumar NAHCON.
Asali: Legit.ng