Hukumar NAHCON Ta Kammala Kwaso Alhazan Najeriya Daga Saudiyya
- Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa NAHCON ta kammala dukkan ayyukan aikin Hajjin 2022 bayan jirgin karshe ya baro Jiddah
- Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya amince da matsalolin da aka samu da kuma matakin da zasu ɗauka a gaba
- Aikin Hajjin Bana ya zo da kalubale da dama ga maniyyata, inda wasu ba su samu damar zuwa ba saboda kurewar lokaci
Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON ta kammala aikin Hajjin bana 2022 bayan jirgin da ya ɗakko sawun ƙarshe na Alhazan Najeriya ya tashi daga filin jirgin saman Sarki Abdul'Azizi da ke Jiddah da misalin karfe 12:00 na dare.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Jirgin mallakin Kamfanin jiragen sama na Azman Air ya ɗakko Alhazai Najeriya 319 daga ƙasar Saudiyya.
Alhazan da suka kasance a sawun ƙarshen sun ƙunshi mahajjatan jihar Kaduna, jihar Kano, da kuma jami'ai daga jihohi da kuma ma'aikatan hukumar NAHCON.
Jirgin Karshen ya taso ne kwanaki shida kafin cikar wa'adin da ƙasar Saudiyya ta sanya wa hukumomi su kwashe Alhazan su daga ƙasar, haka kuma kwana uku kafin wa'adin da NAHCON ta ɗiba na 10 ga watan Agusta ya cika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani bikin murnar kammala Hajjin bana, shugaban hukumar jin daɗin Alhazai NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya gode wa Allah bisa wannan nasara, kana ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa ɗumbin goyon bayan da ta ba su.
An samu matsaloli a Hajjin bana 2022
Shugaban NAHCON ya kuma bayyana tare da amince ws da wasu ƙalubale da aka ci karo da su lokacin kwashe maniyyata daga Najeriya zuwa Saudiyya da suka haɗa da kurewar lokaci da sauran su.
Ya jaddada cewa hukumar zata fara shiri tun wuri kuma zata fara tantance kamfanonin jirage da wuri-wuri domin ba su damar shawo kan duk wasu matsaloli a kan lokaci, Guardian ta ruwaito.
A wani labarin kuma kun ji cewa Wata Mahajjaciya yar Najeriya ta rasa rayuwarta a Saudiyya yayin aikin Hajjin 2022
Wata yar Najeriya da ta yi niyyar aikin Hajjin bana 2022, Hajiya Aisha Ahmad, ta rigamu gidan gaskiya sanadin rashin lafiya a Saudiyya.
Aisha Ahmad, daga ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa , ta rasu ne bayan kamuwa da gajeruwar rashin lafiya, a cewar Alhaji Idris Al-Makura, shugabann hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng