Gwamnonin Najeriya Sun Fadi Hanyoyi Shida Da CBN Ya Lalata Darajar Naira

Gwamnonin Najeriya Sun Fadi Hanyoyi Shida Da CBN Ya Lalata Darajar Naira

  • Gwamnonin Najeriya sun lissafa abubuwa Shida da suka ganin sun jawo faɗuwar darajar Naira a kasuwar duniya
  • Haka nan gwamnonin sun ba shugaban ƙasa shawarwarin da za'a bi don ceto Najeriya daga durkushewar tattalin arziki
  • Gwamnonin sun yi wannan tsokacin ne yayin wata gana wa da shugaba Buhari a watan da ya shuɗe

Abuja - Gwamnonin Najeriya sun yi tsokaci kan dalilan da suke ganin sun haddasa faɗuwar darajar Naira a kasuwar duniya.

Gwamnonin, waɗan da suka nuna damuwarsu kan yadda tattalin arziƙi ke kara tabarbarewa, sun bayyana hasashen su ne yayin gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Gwamnoni da Buhari.
Gwamnonin Najeriya Sun Fadi Hanyoyi Shida Da CBN Ya Lalata Darajar Naira Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa gwamnonin sun shawarci Buhari ya ɗauki wasu matakai kan Babban bankin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

Gwamnonin sun ba da waɗan nan shawarwarin akan babban bankin Najeriya ne bayan sun lura cewa farashin da ake canja Naira ya lalace ne saboda:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. CBN ya gurzo N19trn “hanyoyi da manufofi” domin gwamnatin tarayya saɓani da tsarin bankin na ƙa'ida wanda hakan karya doka ne.

2. Tiriliyoyin Naira na zama a matsayin ƴan biliyoyin daloli, wanda hakan na ƙara matsin lamba akan asusun rarar ajiya da kuma farashin canjin kuɗi.

3. Matsayar CBN ta farashi mara sauyawa kan canjin kuɗi ya hana ƴan ƙasar waje zuba jari inda (a shekarar 2018 ƴan ƙasar waje sun zuba jarin $90bn, yayi ƙasa zuwa $20bn a 2021). Kuma Kuɗin da ƴan Najeriya mazaunan ƙasashen waje ke turowa gida ya ragu daga ($20bn a 2021 zuwa $17bn a 2022)

4. Tallafin man fetur bisa fakewa da 'kasa farfaɗowa' ya cinye kusan ilahirin asusun waje na ajiyar gwamnati.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Gamu Da Ajalinsu Hannun Sojoji Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Kazamin Hari A Jihar Arewa

5. CBN ya koma amfani da yin musanya, da sauran wasu sabbin abubuwa domin ɓoye ainihin kuɗin da ake zara a Asusun waje na Najeriya -Dala Biliyan $36bn da Dala Biliyan $15bn.

6. Tsarin farashin canjin kuɗi yanzu ya koma fifita masu hannu da shuni ta hanyar samar musu da sauƙaƙaƙƙun hanyoyin samun dala, misali neman lafiya a ƙasar waje ($3bn duk shekara), ilmi ($6bn duk shekara) sannan kasuwanci da wasu harkokin kamar su kuɗin hanyar jirage da sauran su ($15bn) a shekarar 2019.

A wani labarin kuma Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

Gwamnonin Najeriya sun shawarci gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta ɗauki wasu matakai cikin gaggawa a wani yunkurin rage wahalhalun kasafin kuɗi da ceto ƙasa daga durkushewar tattalin arziki

Gwamnonin sun gabatar da matakan yayin gana wa da shugaba Buhari a watan da ya shuɗe, rahoton Premium Times ya tabbatar daga wata majiya da bat da ikom faɗin abinda aka tattauna a taron.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262