An kama Wasu ‘Yan Sanda Biyu Da Zargin Cire Wa Wani Dan Kasuwa Makudan Kudi a POS

An kama Wasu ‘Yan Sanda Biyu Da Zargin Cire Wa Wani Dan Kasuwa Makudan Kudi a POS

  • Yan sanda a Legas sun kama wasu mutane biyu da suka yi shigar jami’an su da laifin Cire Wa Wani Dan Kasuwa Makudan Kudi a POS
  • Yan sandan Bogi da suka kai samame gidan wasu samari su biyu sun kwashe musu dalar amurka dubu biyar 5000
  • Daya daga cikin masu laifin da aka kama korarren dan sanda ne wanda ke jagorantar wasu gungun ‘yan fashi a Legas

Jihar Legas - ‘Yan sanda a Legas sun kama wasu mutane biyu da suka yi shigar jami’an su, bisa laifin kutsawa gidan wasu samari biyu, tare da yi musu muguwar duka da kuma amfani da POS, don cire kusan N1.350m daga asusun su. Rahoton VANGUARD

An kuma yi zargin masu laifin sun kwace wa samarin dala 5000 da suka samu a gidansu tare da lalata musu kadarori a lokacin da suka kutsa gidan su.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun shiga wata jihar Arewa, sun hallaka 'yan kasuwa, sun sace matafiya 14

Wadanda abin ya shafa, Fatai Showumi Shina, mai shekaru 20, dilan kayan gyarar mota da Samuel Toyosi, mai shekaru 25, sun ce yansandan bogi sun kai farmaki gidansu da ke lamba 15, titin Oseyintola, Ifako-Ijaiye a Agege, Legas, da misalin karfe 11:30 na dare ranar 15 ga Yuli, 2022.

YANSA
An kama Wasu ‘Yan Sanda Biyu Da Zargin Cire Wa Wani Dan Kasuwa Makudan Kudi a POS FOTO VANGUARD
Asali: Facebook

Yan sandan bogin sun zo tare da mutane bakwai dauke da muggan makamai sanye da kayan yan sanda inda suka ce sun zo, yi musu bincike ne kan zargin suna garkuwa da mutane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga baya suka bayyana kansu a matsayin jami’an ‘yan sanda daga hedkwatar rundunar yan sanda Najeriya daga Abuja.

A cikin biniciken da suka yi sun gano dalar Amurka 5,000 a cikin wata rigar da suka kwashe cikin sauri.

Samarin da abun ya rutsa da su, sun ce yan sandan bogin sun dauke su a cikin mota, suka kai su gaban ofishin ‘yan sanda na Red House, Iju a dake Legas inda aka azabtar da su ba tare da jin ƙai ba.

Kara karanta wannan

Yan Luwadi Shida Sun Shiga Hannu A Nasarawa, Yan Sanda Sun Gargadi Mazauna Jihar

Sun sake fitar dasu zuwa gaban ofishin ’yan sanda na Meran inda aka ci gaba da dukan su har aka tilasta musu bayyana lambar asusun bankin su.

Da suka gano naira milyan N1.7m a cikin asusun Fatai, sai suka yi amfani da katin ATM dinsa suka ciro naira miliyan N1, 350, 000 .00 da shi ta hanyar amfani da injinan POS daban-daban.

Majiyar ‘yan sandan ta ce daya daga cikin wanda ake zargi korarren dan sanda ne wanda yake jagorantar wasu gungun ‘yan fashi ne da suka dade suna gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban a Legas.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama mutanen biyu, ya kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne — Amotekun

Hukumar Tsaro na Yankin kudu maso Yamma mai taken AMOTEKUN ta bayyana cewa babu dan ta’adda guda daya cikin matafiya yan Arewa 170 da ta kama sabanin labarin da ta rawaito a baya. Rahoton Aminiya

Dailytrust Rundunar ta ce ta gano matafiya za su sauka a garin Ogere na Jihar Ogun, don haka za ta mika su ga jami’an rundunar ’yan Sandan jihar, domin yi musu bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel