Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya rasuwa
- Yanzun nan muke samun labarin cewa, Tafa Balogun, daya daga cikin tsifaffin Sufetoci na 'yan sandan Najeriya ya rasu
- Tafa dai ya zama shugaban 'yan sanda, kafin nan kuma ya yi aiki a sassa daban-daban kasar nan a hukumar ta 'yan sanda
- A rahoton da muka samo, an bayyana wasu abubuwan da dama da suka faru bayan barinsa a shekarun baya
Yanzu muke samun labarin cewa, Mustapha Balogun, tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, ya rigamu gidan gaskiya, Vanguard ta ruwaito.
Majiyar iyalansa da ta tabbatar da mutuwarsa, wanda ya zama IGP a watan Maris na 2002, ta ce ya rasu ne a daren ranar Alhamis, amma ba ta yi cikakken bayani akai ba.
An haife shi ne a ranar 8 ga Agusta, 1947 a Ila-Orangun a Jihar Osun, Tafa Balogun, shi ne Sufeto-Janar na 'yan sanda na 21 a tarihin Najeriya.
Kafin zamansa IGP, Tafa ya yi aiki a jihohi daban-daban na Najeriya kana ya rike mukamai da dama a hukumar 'yan sanda har zuwa ritayarsa, rahoton Daily Trust.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar 4 ga Afrilu, 2005, Balogun ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa laifin sata da karkatar da sama da dala miliyan 100 a cikin shekaru uku da ya yi a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda daga baitul malin ‘yan sanda.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gabatar da tuhume-tuhume 70 a kansa.
Amma ya yi yarjejeniya da kotu domin ya mayar da mafi yawan kadarorin da kudaden da ake tuhumarsa a kai. An yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.
IGP Ya Umarci a Zagaye Babban Birnin Tarayya Abuja da Tulin Jami’an Tsaro
A wani yunkuri na kawar da fargabar mazauna Abuja dangane da barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya ba da umarnin tura karin jami’an ‘yan sanda masu yawan gaske zuwa birnin.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an dauki matakin ne domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna, muhimman kadarorin kasa da dai sauran ababe a zagayen birnin tarayya Abuja.
IGP ya ba da wannan umarni ne a yayin taron da rundunar ta gudanar a ofishinsa, yayin da yake samun cikakken bayani kan harkokin tsaro a kasar.
Asali: Legit.ng