'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Babban Malami a Jihar Anambra
- Wasu tsageru sun je har gida sun sace wani babban Malamin addinin kirista a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta arewa, jihar Anambra
- Wasu bayanai da aka tattara sun nuna cewa maharan sun ɗauke malamin ne da tsakar dare bayan ya kammala addu'o'i
- Hukumar yan sanda reshen jihar Anamvra ba tace komai ba game da sabon harin, wata majiya tace tun bayan ɗauke shi ba bu wani labari
Anambra - Wasu mutane ɗauke da bindigu sun yi awon gaba da babban shugaban Mabiya addinin kirista, 'Christian Practical Praying Band,' mai suna, Elder Dan Nwokolo.
Jaridar Punch ta tattaro cewa yan bindigan sun kutsa cikin gidan babban Malamin da ke garin Ufuma, ƙaramar hukumar Orumba ta arewa a jihar Anambra, sannan suka yi gaba da shi.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun sace Malamin ne jim kaɗan bayan kammala ibadar tsakar dare ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta, 2022.
A cewar wata majiya daga yankin, yan bindigan sun tafi da Malamin Addinin Kiristan zuwa wani wuri da ba'a gano ko ina bane a yanzu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika, majiyar ta ƙara da cewa tun bayan ɗauke shi, har yanzun maharan ba su tuntuɓi kowa ba game da garkuwan.
Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, bai ce komai ba don tabbatar da faruwar lamarin kasancewar bai ɗaga kira ko amsa sakonnin da aka tura masa ba har yanzun da muka haɗa rahoton.
Wannan na zuwa ne awanni bayan wasu yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ɗan majalisar dokoki a jihar Anambra, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Matsalar tsaro na ƙara lalacewa a Najeriya duk da barazanar da wasu Sanatoci da yan majalisar dokokin tarayya suka yi na tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Awanni Kaɗan Tsakani, Yan Bindiga Sun Sake Kai Wani Kazamin Hari Kusa Da Babban Birnin Jihar Katsina
Sojoji sun kai wa yan ta'adda farmaki
A wani labarin kuma Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Ta'adda, Sun Halaka Dandazon Su A Jihar Arewa
Rundunar Operation Haɗin Kai ta yi nasarar halaka dandazon mayaƙan Boko Haram a wani samame da ta kai sansanin su da ke Gazuwa.
Wata majiya ta bayyana cewa Soja ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin gwabzawa, yayin da yan ta'adda da yawa suka zama gawa a yankin Bama.
Asali: Legit.ng