Rashin Tsaro: Za Mu Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin an Gudanar da Zaben 2023, In Ji FG
- Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya ya bayyana irin shirin da gwamnain Buhari ke yi na kawo karshen rashin tsaro
- Gwamnati ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa za a yi zaben 2023 lafiya ba tare da wani tsaiko ko tasgaro ba
- Ana ta cece-kuce kan ko Najeriya za ta iya gudanar zabukan 2023 ganin yadda lamurran tsaro suke kara tabarbarewa
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da babban zaben 2023 duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), TheCable ta ruwaito.
A cewarsa, duk da damuwar da ake da ita kan kalubalen tsaro, gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya ta hanyar samar da tsaro da inganta rayuwar jama’a abin da ta fifita kan komai, Daily Sun ta ruwaito.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duk wanda yake da wani ra'ayi yana da 'yancin fadin ra'ayinsa kuma gwamnati za ta auna ra'ayoyin kana ta dauki duk wani mataki da ta yi imanin cewa yana da amfani ga al'umma baki daya.
“Ina tabbatar muku cewa za a yi zabe domin gwamnatin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa ba kawai don tabbatar da an yi zabe ba har ma da tabbatar da tsaron kasar.
“Na tabbata jiya kunji daga bakin shugaban kasa an baiwa kwamandojin soji duk wani abu da suke bukata kuma an basu dukkan ikon da suke bukata domin kawo karshen wannan ta’addanci da ‘yan fashi.
"Game da ko shugabannin tsaro su yi murabus, ina ganin wanda ya nada su ne kawai zai iya yanke shawara a kan hakan, amma shugabannin tsaro sun yi iya kokarinsu kuma za su ci gaba da yin hakan."
Najeriya na fuskantar yawan hare-haren 'yan bindiga a wannan lokaci, lamarin da ke kara dagula zaman lafiya da natsuwar 'yan kasa.
Kusan babu wani gari a Najeriya da rikicin 'yan bindiga bai shiga ba, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi
A wani labarin, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai kasance a tsaka-tsaki a babban zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, yayin da yake jawabi ga yan Najeriya mazauna Portugal a Lisbon, babbar birnin kasar.
Ya kuma bayyana cewa zai ba hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) cikakken yancin gudanar da zabe na gaskiya da amana.
Asali: Legit.ng