Bidiyo: Magidanci ya dawo daga kasar waje, ya tarar matarsa ta siyar da tamfatsetsen gidansa N10m kacal
- Wani 'dan Najeriya da ya je kasar waje ya dawo inda ya tarar da abun rudani a gida saboda ya rasa kadararsa mai muhimmanci
- Mutumin ya gane cewa matarsa ta siyar da tamfatsetsen gidansa kan kudi N10 miliyan kuma sabon mai gidan yana shirin tarewa
- A yayin zagaya gidan, magidancin ya jajanta yadda ya siya filin kadai a N9.5 miliyan kuma ya gina komai da kansa sannan ya ba matarsa amana
Wani magidanci 'dan Najeriya ya koka kan yadda ya dawo daga kasar waje ya gane cewa matarsa ta siyar da tamfatsetsen gidansa kan N10 miliyan.
A wani bidiyon magidancin da ya bayyana cike da takaici kuma ya wallafa a TikTok, an dauka bidiyon yayin da yake zagaya karon gidan.

Asali: UGC
Magidancin da ba a san sunansa ba har a yayin rubuta wannan rahoton, ya bayyana cewa filin kadai ya siye shi kan N9.5 miliyan kuma ya biya dillali N500,000.

Kara karanta wannan
Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta
A yayin nuni da inda gidan yake, yace da kanshi yayi komai tun daga fara ginin, flasta da rufi kafin ya bar kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda yace, ya mika gidan hannun matarsa domin ta lura da shi matsayin amana, alamar dake nuna cewa bai ce mata ta siyar da gidan ba.
Yace an gina gidaje hudu a filin kuma ya bayyana mamakinsa ta yadda har mutum ya yadda ya siye shi a N10 miliyan duk da darajarsa ta fi haka.
Kalla bidiyon a kasa:
Soshiyal midiya sun yi martani
Obalolaofficial yace: "Ba za ta taba ganin cigaba a rayuwarta ba da tayi maka haka. Wannan gidan a N10 miliyan, duk da matarka ce kuma ban san abinda ya faru ba, amma muguwa ce."
Oluchukuwokoye: "Ba jama'a ana neman mace tagari ba, daga bisani sai ta azabtar da mutum."

Kara karanta wannan
Garabasa: Matashi ya sa an yi layi, yana yiwa jama'a aski kyauta saboda kaunar Peter Obi
Gisela Mokoh yace: "Kai, na rasa abinda zan ce. Ya dace ta tafi gidan fursuna kan wannan tare da wanda ya siya. Ina jin irin radadin da kake ji baba."
Kmeter66: "Babu sa hannun ka a yarjejeniyar, don haka zaka iya maka su a kotu kuma ka karbe gidanka."
Norjiboy yace: "Raba mene? Babu laifi ka dinga turo kudi gida. Mutane ne ke auren wawaye. Mata ta ba za ta taba yin irin wannan shirmen ba."
Kamar yana jira: Magidanci ya fara warwasawa da 'yan mata, wata 5 bayan mutuwar matarsa
A wani labari na daban, wata mata ta caccaki tsohon mijin marigayiyar kawarta bayan ya wallafa hotonsa da wata mata a kafar sada zumuntar zamani bayan wata biyar da mutuwar matarsa.
Ma'abociyar amfani da Twitter mai amfani da suna @Miss Roach, ta ce kawarta ta sha wuyar mijinta wanda har wata mata ya dirkawa ciki a lokacin tana da rai.

Kara karanta wannan
Bayan Wuya: Matashi Mai Kafa Daya Wanda Ke Aiki A Wajen Gini Ya Samu Tallafin Karatu A Turai
Ta kara da cewa, kawarta ta karba 'dan mijin wanda ya samu a gaba da fatiha tamkar nata, kuma ta zauna a gidan aurenta har zuwa shekarar da ta gabata inda tace ga garinku.
Asali: Legit.ng