Abin da ya faru a lokacin da KASTELEA suka cafke Yaron Gwamna El-Rufai
- Bashir El-Rufai ya bada wani gajeren labari kan haduwarsa da Jami’an KASTELEA a Kaduna
- Duk da cewa shi yaron Gwamnan jihar Kaduna ne, Bashir El-Rufai ya amsa laifin da ya aikata
- Wannan sako ne ga masu kokarin nunawa jami’an tsaro cewa sun san manya idan an yi ram da su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bashir El-Rufai wanda yana cikin manyan ‘ya ‘yan Gwamnan Kaduna, ya bada labarin wata takaddamarsa da jami’an KASTELEA.
Malam Bashir El-Rufai yake cewa akwai lokacin da jami’an KASTELA masu kula da tituna da motoci suka taba yin ram da shi a hanya.
Kamar yadda ya shaida a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, an kama shi ne saboda ya saba doka.
Duk da yana yaron Mai girma Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Bashir ya amsa laifin da KASTELEA suka kama shi da aikatawa.
A cewarsa, bai tsaya wata-wata ba ko ya yi wa jami’an barazanar zai kira Gwamna a waya, ya biya taran da ya yi daidai da laifin na sa.
Sakon da yake kokarin isarwa shi ne bai dace mutum ya saba doka, sannan ya rika gadara ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Maganar Bashir El-Rufai a Twitter
“A Kaduna, KASTALEA sun taba tare ni saboda saba dokar hanya. Ban ce masu zan kira Gwamnan ba.
Sai na lallaba na biya tarar da aka ci ni kuma na cigaba da harkokin gabana na ranar. Na saba doka ne.
A matsayinmu na ‘Yan Najeriya, ya kamata mu yi watsi da wannan barzana da kokarin nuna mu wasu ne, musamman ‘yan jarida.”
'Dan jarida ya bi titin BRT a Legas
El-Rufai ya yi wannan magana ne biyo bayan abin da ya faru da wani ‘dan jarida da aka kama ya saba doka a titin Legas kwanakin baya.
Wannan mutumi ya yi ikirarin zai kira gwamnan jihar Legas a wayar salula bayan jami’an ‘yan sanda sun karbe motar da yake tukawa.
Daga baya Legit.ng Hausa ta fahimci an gurfanar da ‘dan jaridar a kotun da ke binciken wadannan laifuffuka, ya biya tarar N70, 000.
Asali: Legit.ng