2022: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya

2022: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya

  • A yanzu dai ba sabon labari ba ne cewa yawancin ‘yan Najeriya rayuwa suke hannu baka hannu kwarya saboda tsadar kayan abinci
  • Wasu daga cikin kayan abinci da aka samu sun yi tashin gwauron zabi a shekarar da ta gabata sun hada da abincin da talakawa ke rayuwa a kai
  • Burodi na daga cikin kayan abinci da a yanzu ka iya fin karfin talakan Najeriya saboda tsananin tsadarsa

Karancin albashi da yadda hauhawar farashin kaya ke karuwa a kullum, yana da matukar wahala ka rayu a matsain talaka a Najeriya.

Ba wai kawai farashin abubuwa ba ne ke dagula lissafin talaka tare da gigita kwanciyar hankalinsa, akwai tunanin zuwa kasuwa tare da jin abin tsoro na yadda farashin ke kara shillawa sama.

Yadda kayan abinci ya tashi a Najeriya
2022: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Hukumar Kididdiga ta Kasa kwanan nan ta sanar da cewa hauhawar farashin abinci, wanda galibi ke kayyade ingancin rayuwar ‘yan kasa, ya karu zuwa 20.6% a watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Matsin Rayuwa: Farashin Litar Kalanzir ya kai N800, Ƴan Najeriya sun Shiga Halin Ha'u'la'i

A cewar NBS, hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin burodi da hatsi, sauran kayayyakin abinci irinsu dankali, dawa, da sauransu. Kana da su nama, kifi, mai da mai da kuma barasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu daga cikin abinci guda bakwai na gama-gari da 'yan Najeriya ke fama da wahalar kudinsu a kasuwa.

Burodi

A Najeriya akwai lokacin da mutum zai iya morewa da burodin N50. A yanzu zai yi wuya a samu burodi akan N200, idan aka yi sa’a aka samu, to cike yake da iska.

Wani abin takaicin shine, a ranar 25 ga Yuli, 2022, kungiyar masu yin burodi ta Najeriya ta kara bayyana karin farashin kaya.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa kungiyar ta ce burodin N200 zai koma tsakanin N240 zuwa N250; na N500 zai koma N600; na N600 zai koma N750; N700 zai koma N880, na N800 kuma za koma tsakanin N980 zuwa N1,000.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kayayyaki Ke Cigaba Tashi A Kasar

Shinkafa

Abincin yau da kullun ga talaka shine shinkafa, yanzu yana daya daga cikin kayan abinci masu matukar tsada a Najeriya.

Wani binciken farashi da Legit.ng ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da buhun shinkafa akan kudi N31,000- N33,000 idan aka kwatanta da N8000 da ake sayarwa a shekarun baya.

Yawancin jama'a a Najeriya a yanzu sun yi watsi da tunanin cin shinkafa a matsayin abincin yau da kullum.

Garrin rogo

Kofin garrin rogo ya zama kofin garin zinari. Babu wani abu mai ban tsoro kamar rashin iya samun damar sayen garin rogo; mafi kaskanci a abincin talakan Najeriya.

NBS, a rahotonta na zababbun kayan abinci, ya nuna cewa matsakaicin farashin garrin rogo 1kg ya karu da 29% a watan Yuni zuwa N353.95.

Kifi

Kifi ya zama daya daga cikin kayan abinci mafi tsada a kasuwa a yau.

A ranar Talata ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koka kan yadda tsadar man dizal ya yi wa sana’ar kifi illa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da shugabar matan APC a Kogi ta tsallake harin 'yan bindiga

A cewar Obasanjo, a halin yanzu farashin man dizal kan N800 a kowace lita, kuma ana samar da kilogram na kifi a kan N1,400.

Wannan kai tsaye na nufin farashin kifi zai yi matukar karuwa a kasuwa.

NBS ta sanya matsakaicin farashin kilo daya na daskararren kifin Mackerel 1kg akan kudi N1,459.82 kamar yadda a watan Yunin 2022, wanda ya karu da 23.82% cikin 100% idan aka kwatanta da N1,178.96 a watan Yunin 2021.

Wake

Wake wani nau'in abinci ne da ke kokarin zama sai gidan wane-da-wane ga 'yan Najeriya ba.

Kamar yadda Nairametrics ta bayyana, farashin babban buhun wake ya tashi da 40.4% inda aka sayar da shi kan N66,000 a cikin watan Yulin 2022 idan aka kwatanta da N47,000 da aka sayar a watan da ya gabata na Yuni 2022.

Doya

Doya kam ba ta ma tabuwa domin ta zama dozen zinare ga iyalai da yawa a Najeriya. Saiwar doya mai kyau da a baya kudinta bai wuce N1,413 a yanzu ta kai N2,350.

Kara karanta wannan

Tana Tara Kudi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

Tsadar rayuwa: Jihohin da suka fi ko'ina tsadar gas din girki a Najeriya

A wani labarin, hukumar kididdiga ta kasa ta ce matsakaicin farashin da ake cika tukunyar gas din girki na 5kg ya karu zuwa 3,921.35 a watan Mayun 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton farashin gas na watan Mayun 2022 da hukumar NBS ta saki a shafinta na Twitter.

Hukumar NBS ta ce a kan cika tukunyar ne kan naira 3,800 a watan Afrilun 2022, tana mai cewa karin ya nuna yana tashi da kaso 3.18 cikin dari a wata-wata, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.