Gwamnatin Tarayya Ta Sayawa Jamhuriyar Nijar Motocin Naira Biliyan 1.4
- Gwamantin Buhari ta tabbatar da sayan wa Jamhuriyar Nijar Motoci da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4
- Ministar kasafin kudi Ta ce shugaba Buhari ya ba da umarnin sayar wa kasar Nijar Motoci dan Inganta tsaron kasar su
- Zainab Ahmed ta ce shugaba Buhari na da ikon daukar matakan da za su amfani Najeriya
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta amince da sayen motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4 ga makwabciyarta jamhuriyar Nijar domin magance matsalar rashin tsaro. Rahoton Channels TV
Ministar kasafin kudi, da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ta tabbatar da hakan a ranar Larabar da ta gabata, inda ta bayyana cewa yin kyauta ga makwabciyarta Jamhuriyar Nijar ba sabon abu ba ne, kuma hakkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da siyan.
A cewarta, shugaba Buhari, mutum ne da bazata iya tambayarsa dalilin daukar wasu matakai ba, saboda yana da hakkin yanke shawarar da zai amfani Najeriya.
Ministan wacce tayi magana bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta, ta amsa tambayoyi dangane da wasu takardu da aka fitar a shafukan sada zumunta wadanda suka nuna cewa shugaban ya amince da fitar da kudaden ne a ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 ga Jamhuriyar Niger.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyan albashin watan Yuli
A wani labari kuma, A daren ranar Talata wasu jami’an sojojin Najeriya da suka hada da na ruwa, kasa da na sama suka yi korafi kan jinkirin da gwamnatin tarayya ta yi na biyan su albashin watan Yuli. Rahoton PUNCH
Batun rashin tsaro: Sanatocin Najeriya sun hado kan shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, suna ganawa
Wasu Sojoji mazauna Abuja da suka zanta da wakilan jaridar PUNCH wanda suka nemi a sakaya sunansu sun ce, su da takwarorinsu ba su ji dadin yadda gwamnatin shugaba Buhari tare da hafsoshi suka ki biyan su albashin watan Yuli ba.
Asali: Legit.ng