Kamfanonin Hada Motoci Hamsin Da Biyu 52 Sun Durkushe A Najeriya

Kamfanonin Hada Motoci Hamsin Da Biyu 52 Sun Durkushe A Najeriya

  • Kamfanonin hada motoci shida kadai suka rage suna aiki a Najeriya daga cikin kamfanoni 52 da aka baiwa lasisin aiki a shekarar 2015
  • Rashin sanya hannun Buhari a kan Kudurin Dokar Bunkasa Bangaren Motoci Na Kasa (NAIDP Bill) yana cikin kalubalen da kamfanonin hada motoci suka fuskanta a Najeriya
  • Mataimakin shugaban Kamfanin Motoci na CFAO ya ce shigo da motoci daga kasashen waje ya fi hada su a Najeriya saukin kudi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamfanonin hada motoci shida kadai suka rage suna aiki a Najeriya daga cikin kamfanoni 52 daga shekara 2015 zuwa yanzu. Rahoton Aminiya.DAILYTRUST

Gwamnatin shugaba Buhari ta bai wa kamfanonin hada motoci 58 lasisin kerawa da hadawa a shekarar 2015 karkashin wani shiri mai taken samar da motoci a cikin gida (NADDC).

Kara karanta wannan

Jiragen Kasan Legas-Kano da Ajaokuta Sun Daina Aiki Bayan Harbin wasu Fasinjoji

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa masu zuba hannun jari sun sanya sama da Dala biliyan daya a karkashin shirin, wanda zai fara da shigo da sassan da kuma kayan motoci (SKD) domin hadawa a cikin gida kafin daga bisani a fara kerawa (CKD) a Najeriya.

Naija
Kamfanonin Hada Motoci Hamsin Da Biyu 52 Sun Durkushe A Najeriya FOTO Naija Auto.com
Asali: UGC

Mataimakin shugaban Kamfanin Motoci na CFAO, Mista Kunle Jaiyesinmi, ya ce a yanzu dai kamfanoni hada motoci a Najeriya guda shida kadai suka rage duk sauran sun daina aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kin rattaba hannun Buhari a kan Kudurin Dokar Bunkasa Bangaren Motoci Na Kasa (NAIDP Bill) yakara kawo wa bangaren cikas.

Kunle ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da yan jaridar kan wani shirin makomar masana’antar motoci a Najeriya.

Sauran sun hada da tafiyar hawainiya wajen tantance kwantainonin a tashar jirgin ruwa.

Kunle ya ce a yanzu dai shigo da motoci daga kasashen waje ya fi hada su a Najeriya saukin gaske.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IGP ya gayyaci kwamishinonin 'yan sanda a wata ganawa don dinke matsalar tsaro

An kama Wasu ‘Yan Sanda Biyu Da Zargin Cire Wa Wani Dan Kasuwa Makudan Kudi a POS

A wani labari kuma Yan sanda a Legas sun kama wasu mutane biyu da suka yi shigar jami’an su, bisa laifin kutsawa gidan wasu samari biyu, tare da yi musu muguwar duka da kuma amfani da POS, don cire kusan N1.350m daga asusun su. Rahoton VANGUARD

An kuma yi zargin masu laifin sun kwace wa samarin dala 5000 da suka samu a gidansu tare da lalata musu kadarori a lokacin da suka kutsa gidan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa