Yanzu-Yanzu: Sanatocin Najeriya sun shiga ganawa da shugabannin hukumomin tsaro
- Shugabancin majalisar dattawa ta shiga ganawar tattaunawa kan batun tsaro da shugabannin hukumomin tsaro na Najeriya
- A makon da ya gabata ne majalisar dattawa ta yi barazanar tsige shugaban kasa muhammadu Buhari idan ya gaza magance tsaro
- Ana kyautata zaton zaman yau a majalisar zai yi duba ga yadda za a magance matsalolin kasar nan
A halin yanzu dai shugabancin majalisar dattawan Najeriya na cikin wata tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaron kasar.
An fara ganawar ne ‘yan mintoci kadan bayan karfe 2:00 na rana a harabar majalisar dattawa ta kasa a ranar Laraba, Punch ta ruwaito.
Wasu Sanatocin da suka halarci taron sun hada da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Wamakko da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojojin Ruwa, George Sekibo.
Hakazalika da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Abdullahi DanBaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A lokacin hada rahoton, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba duk da cewa an lura da cewa ya zo harabar karfe saura mintuna 15 cikin tsauraran matakan tsaro.
Rahoton jaridar ya kuma ce, sai da aka jinkirta taron don jiran zuwansa.
Ku tuna cewa ‘yan majalisa karkashin kugiyar marasa rinjaye sun baiwa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), wa’adin makwanni shida ya warware matsalar rashin tsaro a kasar ko kuma su tsige shi.
Maganar Ahmad Lawan gabanin ganawar
Kafin ganawar ta sirri, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya shaidawa jami’an tsaro cewa matsalar rashin tsaro na da ban tsoro a Najeriya.
A cewar Lawan, babu wani abu da ya nuna cewa irin dimbin kudade da ake zubawa a harkar tsaro na haifar da da mai ido, inji rahoton jaridar Vanguard.
A wani labarin, a ranar Litinin ne dimbin mazauna Abuja suka yi dandazo a dandalin Unity Fountain na birnin domin nuna rashin amincewarsu da karuwar rashin tsaro da rashin tabuka komai daga jami’an tsaro wajen dakile ta’addancin garkuwa da mutane.
Babban birnin tarayya Abuja ya shiga sahun wuraren da ke fama da yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a cikin shekarar nan, inda aka samu munanan hare-hare da dama, This Day ta ruwaito.
Da suke jawabi a karkashin kungiyar masu kula da harkokin dimokaradiyya ta GDDI, matasan da suka fusata sun yi mamakin dalilin da ya sa duk da rahotannin sirri da aka samu na wasu shirye-shiryen kai hare-hare a Abuja, har yanzu ba a samu mafita ba.
Asali: Legit.ng