Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne — Amotekun
- Hukumar Tsaro na Yankin kudu maso Yamma mai taken AMOTEKUN ta bayyana cewa babu dan ta’adda guda daya cikin matafiya yan Arewa 170 da ta kama
- Kanal Olayinka Olayaju ya ce yunkurin guduwa da wasu daga cikin matafiyar yan Arewa suka yi a lokacin da suka jami'an Amotoken ya sa aka kama su
- Hukumar Amotekun zata mika matafiya yan Arewa da ta kama ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun saboda can suka nufa
Jihar Ondo - Hukumar Tsaro na Yankin kudu maso Yamma mai taken AMOTEKUN ta bayyana cewa babu dan ta’adda guda daya cikin matafiya yan Arewa 170 da ta kama sabanin labarin da ta rawaito a baya. Rahoton Aminiya.Dailytrust
Rundunar ta ce ta gano matafiya za su sauka a garin Ogere na Jihar Ogun, don haka za ta mika su ga jami’an rundunar ’yan Sandan jihar, domin yi musu bincike.
Shugaban Hukumar Amotekun reshen Jihar Oyo, Kanal Olayinka Olayaju, ya bayyana wa manema labarun jaridar Aminiya cewa da farko jami’an Amotekun ba su niyyar kama su ba a lokacin da suka hango ayarin matafiyan, amma kokarin tserewar da wasu daga cikin su suka yi ya sa aka kama su.
Kanal Olayinka Olayaju, yace “Mutanen sa sun sanar da shi yadda kusan mutum 20 daga cikinsu suka gudu da suka hango su, wannan ne ya sa suka yi zargin ko ’yan kungiyar Boko Haram ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma yanzu za a mika su ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, tunda sun ce can suka nufa inji Kanal Olayinka Olayaju,
Yan Bidiga Da Ake Zargi yan Kugiyar IPOB ne Sun Budewa Yan Arewa Wuta Jihar Imo
A wani labari kuma, Mutanen yankin arewacin Najeriya da ke zaune a Jihar Imo, suna cikin fargaba da tashin hankali yayi da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari a jihar Imo. Rahoton BBC
Yan Bindigan da ake zargi yan Kungiyar IPOB ne, sun halaka akalla mutane 6 shida, tare da raunata mutane da yawa.
Asali: Legit.ng