Yaron Da Ya Kashe Hannu Da Zulum Ya Samu Dankareren Hotonsa Hannunsa Rike Da Na Gwamnan
- An gabatarwa wani dan karamin yaro da ya sha hannu da gwamnan jihar Borno dankareren hoton wannan lokaci mai dumbin tarihi
- A cewar wata wallafa da CBN Gov Akinsola Akin ya yi a Twitter, hadimin gwamnan ne ya gabatarwa da yaron babban kyautar
- An tattaro cewa yaron ya yi musabaha da gwamnan ne a hanya yayin da yake wucewa da ayarinsa
Wani karamin yaro da ya yi musabaha da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya samu an gabatar masa da dankareren hoton lokacin.
Sai dai kuma masu sharhi sun ce mutumin da ke cikin ayarin motocin ba Zulum bane face mataimakin gwamnan domin motar alfarmar na dauke da rubutun “mataimakin Gwamna” baro-baro.
Yaron zai hadu da Gwamna Zulum
Sai dai, wani mai fada aji a Twitter, CBN Governor Akinsola ya dage cewa yaron ya samu babban hoton ne daga wajen hadimin gwamnan kuma zai gana da shi kwanan nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar 2 ga watan Agusta, 2022, Akinsola ya yada hotunan yaron rike da dankareren hoton.
Sai dai Legit.ng ba ta tabbatar da ko gwamnan ne a cikin motar ba da kuma wanda ya sha hannu da yaron, amma rahotannnin da ke yawo a shafukan soshiyal midiya sun ce Zulum ne ya sha hannu da wasu mazauna yankin.
Daga cikin hotunan ne aka gabatarwa yaron da nashi kuma an gano shi yana rike da shi cike da farin ciki a unguwanni yayin da yake alfahari da hakan.
A cikin wani hoton, an gano yaron rike da katafaren hoton yayin da mutane da dama suka zagaye shi a kan titi. Ya kuma rataya hoton a cikin daki cike da alfahari.
Sabbin Hotunan Gwamnan Jihar Neja Yana Tuka Babur Sun Bayyana
A wani labarin, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi abun da ba’a saba gani ba daga gare shi.
An dai gano Gwamna Bello yana tuka babur a cikin wasu sabbin hotuna da ya bayyana a shafin soshiyal midiya.
Shafin gwamnatin jihar Neja ce ta wallafa hotunan a Twitter a ranar Talata, 2 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng