Yan Bindiga Da Ake Zargi yan Kungiyar IPOB ne Sun Budewa Yan Arewa Wuta a Jihar Imo
- Mutanen yankin arewacin Najeriya da ke zaune a Jihar Imo, suna cikin fargaba da tashin hankali yayin da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari a jihar Imo
- Rundunar Yansanda Najeriya reshen jihar Imo ta lashi takobin gano wadanda suka kai wa yan Arewa hari a jihar Imo
- Wani Alhaji Hamza ya ce yan bindigan da suke budewa yan Arewa wuta sun fille wa mutun daya kai kuma sun tafi dashi
Jihar Imo - Mutanen yankin arewacin Najeriya da ke zaune a Jihar Imo, suna cikin fargaba da tashin hankali yayin da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari a jihar Imo. Rahoton BBC
Yan Bindigan da ake zargi yan Kungiyar IPOB ne, sun halaka akalla mutane 6 shida, tare da raunata mutane da yawa.
Wannan mummunar al’amari ya faru ne da misalin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na cikin dare ranar Litinin 2 ga Watan Yuni 2022 a garin Ubaku dake Ƙaramar Hukumar Owerri ta yamma.
Sai a ranar Talata aka samu damar dauko gawarwakin wadanda aka kashe sa'annan aka yi jana'izarsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Imo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta dau alwashin kamo wadanda suka aikata laifin.
Daya daga cikin shugabanin yan Arewa mazauna jihar Imo, Alhaji Hamza Abdullahi, ya ce yan bindigan sun zo ne sanye da kayan jami’an sojoji inda suka zauna tare da su, sai mutanen wurin suka ba su shayi domin girmama su.
Alhaji Hamza ya ce bayan sun kammala shan shayin sai suka kama hanya za su tafi daganan suka juyo suka bude musu wuta da bindiga.
Yan Bindigan sun cire kan mutum guda suka tafi da shi, bayan haka akwai akalla mutane bakwai da suka jikkata a asibiti.
Alhaji Hamza ya ce babu wanda suke zargi da zuciyar kai irin wannan hari kamar kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biyafra.
Addini Ba Zai Hana Kiristocin Arewa Zaben Tikitin Musulmi da Musulmi ba – Osita Okechukwu
A wani labari kuma, Darakta Janar na Hukumar Muryar Najeriya VON, Osita Okechukwu, ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan muhimmancin cancanta kan addini ko kabilanci a zaben 2023. Rahoton Arise News
Osita Okechukwu,ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC yana da basira da kwarewar tunkarar kalubalen da ke gaban shi na shugabanci Najeriya.
Asali: Legit.ng