Sabbin Hotunan Gwamnan Jihar Neja Yana Tuka Babur Sun Bayyana
- Wasu sabbin hotuna sun bayyana a shafin soshiyal midiya inda aka gano Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, yana tuka babur
- Gwamna Bello ya kaddamar da hukumar kula da ababen hawa na jihar Neja wato NISTMA
- Tuni mabiya shafukan soshiyal midiya suka bayyana ra’ayoyinsu game da muhimmancin wannan hukuma
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi abun da ba’a saba gani ba daga gare shi.
An dai gano Gwamna Bello yana tuka babur a cikin wasu sabbin hotuna da ya bayyana a shafin soshiyal midiya.
Shafin gwamnatin jihar Neja ce ta wallafa hotunan a Twitter a ranar Talata, 2 ga watan Agusta.
Sai dai kuma, bayanan da ke tattare da hotunan ya nuna gwamnan ya tuka babur dinne a wajen kaddamar da hukumar kula da ababen hawa ta jihar Neja wato NISTMA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli hotunan a kasa:
Jama'a sun tofa albakacin bakunansu
@mubarak37137751 ya yi martani:
“Bana tunanin muna bukatar wannan a yanzu. Babban abun da ya kamata a inganta shine tsaro a jihar. Ku tanadi yan CJTF masu kayayyaki a kowace karamar hukumar jihar. Wannan zai fi inganci. Ra’ayina.”
@Ibnwalee ya ce:
“Bana tunanin muna da matsalar cunkoso da zai bayar da damar kafa wannan hukuma. Hakan kashe kudi kawai zai karawa gwamnati. Menene aikinsu ma, kuma ta yaya za su yi aiki tare da FRSC?”
@katchali ya yi martani:
“Shin wannan ne abun da mutane ke bukata a irin wannan lokaci? Wa ke ba mutanen nan shawarwari ne?”
Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane
A wani labarin kuma, kamar yadda yake a bisa al’adar mutanen arewacin kasar, musamman ma a tsakanin al’ummar Hausawa ba a cika samun mata suna wasu ayyuka da maza ke yi ba.
Misali da wuya a ga mace tana tuka achaba, adaidaita, dako da sauran ayyukan karfi. A al’adance, Bahaushe ya fi son matarsa ta zama a cikin gida.
Sai dai kuma wata mata mai matsakaicin shekaru ta sauya wannan tunani inda ta kama sana’ar tuka adaidaita sahu.
Asali: Legit.ng