Tashin hankali yayin da shugabar matan APC a Kogi ta tsallake harin 'yan bindiga

Tashin hankali yayin da shugabar matan APC a Kogi ta tsallake harin 'yan bindiga

  • An samu hargitsi yayin da wasu 'yan bindiga suka kutsa kai cikin gidan wata tsohuwar jigo a jam'iyyar APC
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun harbi Hajiya Ageji Omale lokacin da take kwance cikin gida
  • Ana yawan samun tashe-tashen hankula a kasar nan duk da cewa kasar na fuskantar zaben shekarar 2023

Jihar Kogi - Tsohuwar shugabar mata a jam’iyyar APC mai mulki a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, Hajiya Ageji Omale ta tsallake rijiya da baya a wani harin da aka kai mata.

Rahotanni sun ce an kuskure ta ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, rahoton PM News.

An ce maharan sun kutsa kai cikin gidanta ne da ke Abejukolo-Ife, hedikwatar karamar hukumar lokacin da take barci.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ana ta batun hana acaba, FRSC za ta fara kame wasu nau'ikan babura a Najeriya

Yan bindiga sun kuskuri jigon APC a jihar Kogi
Tashin hankali yayin da shugaban matan APC a Kogi ta tsallake harbin bindiga | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: Twitter

Daga baya ‘yan bindigar da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun gudu suka bar ta a kwance jini.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kukan da ta yi na neman agaji ne ya ja hankalin makwabta inda daga baya suka garzaya da ita ofishin ‘yan sanda domin ba da rahoto kafin a kai ta babban asibitin Abejukolo domin kula da lafiyarta.

Daya daga cikin makwabtanta ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar makwabcin nata

"Dukkanmu muna cikin gida, kana wasu mazauna da yawa suna can gonakinsu lokacin da muka ji karar harbe-harbe kuma daga baya muka ji muryar Mama tana ihu mai karfi. Maharan ta sun gudu kafin isowar mu.
“Mun yi mamaki domin Hajiya macece mai son zaman lafiya kuma uwa ga kowa da kowa. Muna rokon ‘yan sanda su fatattaki 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu domin hakan yana nufin ba mu da tsaro a cikin gidajenmu.”

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun shiga wata jihar Arewa, sun hallaka 'yan kasuwa, sun sace matafiya 14

Kokarin jin ta bakin jami’in ‘yan sanda reshen Omala ta wayar salulu ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sabon Hari: 'Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 4, Sun Sace Matafiya 14 a Taraba

A wani labarin, akalla mutane hudu ne suka mutu a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga kimanin 30 a kan babura suka mamaye kasuwar Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol inda suka bude wuta kan wasu ‘yan kasuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ce sun kuma yi awon gaba da mutane shida yayin da ‘yan kasuwa suka bar hajojin su, suka gudu zuwa wani daji da ke kusa.

Wani mazaunin garin Umar Tasiu ya shaida wa jaridar cewa harin na ranar Lahadi shi ne na uku da aka kai garin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.