Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sako karin mutum 5 daga fasinjojin jirgin kasan Abj-Kad
- Bayan shafe watanni a hannun 'yan bindiga, fasinjoji biyar daga sun samu 'yanci daga sansanin 'yan ta'adda
- Watanni da suka gabata ne aka samu mummunan harin 'yan bindiga a kan titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
- Ya zuwa yanzu, an sako mutum 37, yayin da wasu 35 ke ci gaba da fuskantar tasku a hannun tsagerun
Kaduna - Yanzu muke samun rahoton da ke cewa an sake sakin wasu fasinjoji biyar da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Ya zuwa yanzu, an sako akalla mutane 37, wanda kuma har yanzu akwai sauran 35 da ke tsare a hannun 'yan bindiga, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.
Daga cikin fasinjojin da aka saki akwai Farfesa Mustapha Umar Imam, likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sokoto.
Rahoton Daily Trust ya ce an harbi Farfesa Imam a lokacin da yake, lamarin da ya haifar da damuwa game da lafiyarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran fasinjojin da aka sako sun hada da Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Muktar Shuaibu da Sidi Aminu Sharif.
Mawallafin jarida a Kaduna, Tukur Mamu, wanda da kansa ya shiga tattaunawar don ganin an sako mutanen amma ya ja baya saboda wata barazana, ya tabbatar da sakin su a ranar Talata.
Kawo yanzu dai babu tabbas ko an biya kudin fansa ga 'yan bindigan.
An tattaro cewa iyalan kowane daya daga cikin shida da aka sako a baya sun biya Naira miliyan 100 yayin da 'yan bindigan suka karbi kudin fansar wani dan Pakistan a kan Naira miliyan 200.
Tashin hankali yayin da shugabar matan APC a Kogi ta tsallake harin 'yan bindiga
A wani labarin, tsohuwar shugabar mata a jam’iyyar APC mai mulki a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, Hajiya Ageji Omale ta tsallake rijiya da baya a wani harin da aka kai mata.
Rahotanni sun ce an kuskure ta ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, rahoton PM News.
An ce maharan sun kutsa kai cikin gidanta ne da ke Abejukolo-Ife, hedikwatar karamar hukumar lokacin da take barci.
Asali: Legit.ng