Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

  • Joseph Ekala matashi ne mai shekaru 27 da ya halaka kawar kanwarsa ta hanyar shake mata wuya har ta sheka barzahu
  • Matashin ya sanar da yadda rikici ya hada su kan Naira dubu hamsin wacce ta bashi ya juya mata amma ya kashe
  • Bayan sun fara fada kuma ya fahimci ya aika ta lahira, sai ya haka dakinsa ya birne gawarta a karkashin kasa, yace yayi nadama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yenagoa, Bayelsa - Mazauna Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa sun shiga rashin hankali da rudani lokacin da labari ya riske su kan cewa, Joseph Ekala mai shekaru 27 ya halaka kawar kanwarsa, Kate, mai shekaru 25 kuma ya birne gawarta a wani kabari mara zurfi a gidansa.

Taswirar Bayelsa
Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Vanguard ta ruwaito cewa, a yayin zantawa da wanda ake zargin tare da wasu mutum 13 a hedkwatar 'yan sandan jihar a ranar Litinin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat yace:

Kara karanta wannan

Wasu Yan Kasar Afghanistan Sun Bayyana Shakku Akan kisar Al-Zawahiri Da Amurka Tayi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daya daga cikin rahotanni mara dadi da muka samu a cikin ranakun karshen mako shi ne yadda wani matashi ke da hannu wurin halaka budurwa mai shekaru 25.
"A ranar 29 ga watan Yulin 2022, mun samu rahoto daga al'umma Okaka na cewa wani Joseph Ekala mai shekaru 27 ya halaka wata Kate Ugu mai shekaru 25 sakamakon shaketa da yayi kuma ya birne ta a gidansa.
"Jami'anmu sun bazama zuwa wurin da abun ya faru kuma tare da taimakon masana kiwon lafiya aka fito da gawar tare da kai ta ma'adanar gawawwaki domin bincike."

Yadda lamarin ya fara

"Ina aiki a kamfanin samar da man fetur da iskar gas dake Fatakwal. A ranar 1 ga watan Yuli na zo Bayelsa saboda wasu ayyuka a cikin gidana. Kate ta same ni a watan Fabrairu cewa tana bukatar inda zata zauna.

Kara karanta wannan

Bayan Wuya: Matashi Mai Kafa Daya Wanda Ke Aiki A Wajen Gini Ya Samu Tallafin Karatu A Turai

"Gidana daki biyu ne, sai na bata daki daya tunda kawar kanwata ce. Ta sameni kan cewa tana son fara kasuwanci tunda ta san ina yi a baya," yace.

Matashin yace zai koya mata inda ta tura masa N50,000 amma tace tana son ribar N20,000 duk wata. Yace bai amince ba zai mayar mata da kudin ta.

Daga bisani bai mayar da kudin ba ya kashe, lamarin da ya fusatata har ta dinga sanarwa abokan aikinsa cewa 'dan damfara ne.

Kamar yadda yayi bayani, ya dawo gida domin su sasanta amma fada ya shiga tsakaninsu har ya shake ta ta rasu.

Ya haka kabari a tsakiyar dakinsa inda ya birne gawarta.

Kamar yana jira: Magidanci ya fara warwasawa da 'yan mata, wata 5 bayan mutuwar matarsa

A wani labari na daban, wata mata ta caccaki tsohon mijin marigayiyar kawarta bayan ya wallafa hotonsa da wata mata a kafar sada zumuntar zamani bayan wata biyar da mutuwar matarsa.

Kara karanta wannan

Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2

Ma'abociyar amfani da Twitter mai amfani da suna @Miss Roach, ta ce kawarta ta sha wuyar mijinta wanda har wata mata ya dirkawa ciki a lokacin tana da rai.

Ta kara da cewa, kawarta ta karba 'dan mijin wanda ya samu a gaba da fatiha tamkar nata, kuma ta zauna a gidan aurenta har zuwa shekarar da ta gabata inda tace ga garinku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng