Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba

  • Wata matashiya yar Amurka mai suna Nikita Crump ta bayyana yadda rayuwa a cikin mota yake
  • Dole ta sa Crump komawa cikin motarta kirar Honda Civic da zama don ba za ta iya biyan kudin haya, siyan abinci da sauransu ba
  • Tuni ta kafa wani tsari na mayar da motarta wajen baccinta da daddare, tana mai cewa tana yawo daga wannan garejin zuwa wani don gudun zargi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nikita Crump, wata yar Arewacin Carolina mai mabiya sama da miliyan 1 a TikTok ta ba da labarin yadda take gudanar da rayuwarta a cikin mota.

A bisa ga rahoton New York Post, matar ta yanke shawarar komawa cikin motarta kirar Honda Civic da zama bayan gwagwarmayar da take sha na biyan kudin haya kan lokaci da tsallake cin abinci don tara kudi.

Kara karanta wannan

Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki

Nikita
Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Koma Rayuwa Cikin Motarta Saboda Ba Za Ta Iya Biyan Kudin Haya Ba Hoto: Nikita Crump.
Asali: UGC

Hakan na faruwa duk da tarin basussukan da ke kanta yayin da take ayyuka guda biyu.

Crump ta tanadi matakan tsaro

Crump ta fara rayuwa a cikin Hondanta a karshen shekarar 2019 kuma ta yanke shawarar ci gaba da zama a ciki na dan lokaci saboda tsadar rayuwa yayin da farashin abubuwa ke kara yin sama a fadin duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, matashiyar matar ta bayyana matakan tsaron da ta tanada don tabbatar da ganin cewa bata yiwa kanta ko wasu illa ba.

Misali shine labulen tagogin da take amfani da su da daddare sun hana ganin komai daga ciki, abun da tace yana da tasiri sosai wajen bayar da kariya da hana sata.

"Yana da cikakken tsari. Babu wanda ya san ina nan," in ji ta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Da kudin budurwa ta tafi dakin saurayi, ya toshe kiran ta yayin da take hanyar zuwa

Tana bacci a wuraren ajiye mota daban daban

Don gudun kada a gane ta, Crump na yawo daga wannan wajen ajiye motar zuwa wani duk dare.

Tana amfani da manhajar Google Maps wajen gano inda ya fi mata sannan ta binciki motoci nawa ake ajiya a unguwanni da daddare.

Wannan na biyo bayan tukin da take yi da daddare don neman wajen yada zango, ta ajiye motar sannan ta yi kokarin sajewa da wajen.

Idan gari ya waye, sai Crump ta nannade gadonta a kujerar baya sannan ta cire labulen tagogin kafin ta nemi wajen yin wanka.

Crump ta saba da yanayi mara dadi

Motar na da dan karamin faranti ta baya wanda shine ya zama teburin cin abincinta.

Yawancin abun da take ci daga wajen siyar da abinci ne, inda take kai kayanta masu datti wajen wanki mafi kusa domin a tsaftace mata su.

“Ga abubuwan da ke cikin motata da ke da amfani a rayuwar mara muhalli,” in ji ta, tana mai cewa akwai wuraren ajiya a motarta da dan karamin abun chajin kayan wutanta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na Shirin Kara Haraji, Farashin Yin Waya a Salula Zai Tashi

Crump, wacce ta bayyana cewa bata da matsuguni tunda ta san ciwon kanta, ta bayyana cewa ta saba da yanayi na matsi.

Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

A wani labari na daban, jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mai daukar hankali a kafafen sada Zumunta ta Instagram, Sayyada Sadiya Haruna, ta gwangwaje mahaifiyarta.

Sadiya ta dankarawa mahaifiyar tata wani katafaren gida domin ta more tare da cin ribar haihuwarta da tayi.

Sau da dama jarumar ta sha fitowa tana bayyana irin soyayyar da take yiwa mahaifanta musamman ma mamar tata, sannan ta sha cewa a kullun cikin yi mata addu’a suke don haka ita ma take son farin cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng