An Dawo Da Dokar Takaita Zirga-Zirga a Katsina Saboda Barazanar 'Yan Ta'adda

An Dawo Da Dokar Takaita Zirga-Zirga a Katsina Saboda Barazanar 'Yan Ta'adda

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta Jihar Katsina ta sake dawo da dokar takaita zirga-zirgan babura a kananan hukumomin jihar
  • Sanarwar da kakakin yan sanda SP Gambo Isah ya fitar ta ce a birnin Katsina dokar zata rika aiki daga 10 na dare zuwa 6 na safe a kananan hukumomi da ake yawan kai hare-hare kuma 6 na yamma zuwa 6 na safe
  • Dama gwamnatin jihar ta dage dokar takaita zirga-zirgan ne watanni hudu da suka gabata saboda azumin watan Ramadan yanzu kuma an dawo da shi saboda tsaurara matakan tsaro

Jihar Katsina - Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta sake takaita amfani da babura a jihar daga 6 na safe 10 na dare saboda kallubalen tsaro a jihar, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ana ta batun hana acaba, FRSC za ta fara kame wasu nau'ikan babura a Najeriya

Gwamnatin jihar ta dage dokar ne watanni hudu da suka gabata saboda saukakawa mutane zirga-zirga a lokacin azumin watan Ramadan amma aka sake dawo da shi bayan samun bayanan sirri cewa yan ta'adda na shirin kawo hari jihar.

Taswirar Jihar Katsina.
Tsaro: Ƴan Sanda Sun Sake Taƙaita Zirga-zirgan Babura A Katsina. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai magana da yawun yan sandan Jihar, SP Gambo Isah wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a madadin Kwamishinan yan sanda, Idris Dauda Dabban ta ce:

"Ana sanar da al'umma cewa har yanzu dokar hana zirga-zirga da babura daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe tana nan a birnin Katsina. Yayin da a kananan hukumomi da ake yawan samun hare-hare kuma daga 6 yamma zuwa 6 na safe."

Idan za a iya tunawa a cikin wata takardar tsaro da ta fito mai dauke da kwanan wata na 25 ga watan Yulin 2022, Hukumar Tsaro ta NSCDC, ta umurci dukkan rassanta su kasance cikin shiri bayan samun bayanan sirri cewa yan ta'adda na kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na shirin kai hari a Abuja, Legas, Katsina, Zamfara, Kaduna da Kogi.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: DSS Ta Kama Shugaban Boko Haram a Ogun

Hukumar DSS Ta Kama Shugaban Boko Haram a Ogun

A wani rahoton, kun ji cewa ana zaman dar-dar a Abeokuta, Jihar Ogun, a ranar Lahadi, bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.

Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ce ta kama wanda ake zargin kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Wata majiya kwakwara ta shaida wa Daily Trust cewa an kama wanda ake zargi shugaban ne a Boko Haram din a unguwar Ijaye a Abeokuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164