Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Shirya Addu'a Ta Musamman

Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Shirya Addu'a Ta Musamman

  • Gwamnatin Jihar Ƙatsina ta shirya taron Addu'a na musamman a dukkan sassan jihar don neman Allah ya kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Gwamna Masari, yayin jawabi a wurin taron, ya gode wa Malaman da suka halarci wurin don ba da gudummuwarsu
  • Manyan Malamai sun yi kira ga mutane su ji tsoron Allah kuma su cigaba da Addu'ar neman taimakon Allah

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta shirya taron Addu'a na musamman domin rokon albarkar Allah, falalarsa da kuma neman ya kawo ɗauki kan ƙalubalen tsaro da ya addabi jihar da ƙasa baki ɗaya.

Sheikh Abidu Yazid, shugaban kwamitin shirya taron ne ya bayyana haka a wurin taron Addu'ar wanda ya gudana a Katsina ranar Litinin, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Taron Addu'a na musamman.
Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Shirya Addu'a Ta Musamman Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sheikh Yazid ya ce gwamnati ta shirya zaman Addu'an ne domin gode wa Allah SWT bisa ni'imomi da falalarsa, kana kuma a roke shi ya kawo ɗauki a matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

Ya ce Allah ya jarabci mafi yawan Manzanni da mutanen da suka gabace mu da azaba kala daban-daban a lokuta mabanbanta kuma suka yi nasarar tsallake wa, don haka ya yi Addu'ar Najeriya ta tsallake.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko a jawabinsa, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya gode wa Malaman Addinin Musulunci waɗan da suka ba da lokacin su suka halarci zaman addu'ar.

Gwamna Masari ya roki ɗaukacin al'umma su kasance masu rokon Allah SWT ya kawo musu ɗauki a kowane hali suka tsinci kansu.

Manyan Malamai sun yi nasiha

Manyan Malamai da suka halarci taron sun yi Addu'ar Allah ya kawo ƙarshen rashin tsaron da ya dabaibaye jihar Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya.

Sun kuma yi wa mutane nasiha su ji tsoron Allah maɗaukakin Sarki kuma kar su gajiya su cigaba da neman ɗaukin Allah a addu'o'in su.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Yi Garkuwa Da Wasu Shararrun Jaruman Fina-Finai A Najeriya

Zaman Addu'ar makamanciyar wannan ta gudana a dukkan ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar tare da wacce aka gudanar a Katsina, babban birnin jihar.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar, ya samu halartar wurin taron Addu'a domin neman taimakon Ubangiji, kamar yadda Sunnews ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Sokoto, Bello Yabo, yayi addu'ar Allah ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari , gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da 'yan ta'adda.

Bello Yabo ya koka da yadda 'yan Najeriya ke ciki saboda gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262