Gwamna Tambuwal Ya Gana Da Tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo a Abeokuta
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta
- Bayanai sun tabbatar da cewa Tambuwal ya isa gidan Obasanjo da tsakar rana kuma sun sa labule a sirrance
- Wata sanarwa da Ofishin gwamnan ya fitar ta ce tawagar Tambuwal sun ci abinci a gidan daga bisani suka wuce Masallaci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ogun - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a ranar Lahadi ya kai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasajo ziyara a wani yanayi da za a iya kwatanta shi da ganawa kan lamurran kasa.
Taron da aka yi a katafaren gidan tsohon shugaban kasan dake garin Abeokuta na jihar Ogun, ya kasance na sirri, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A wata takardar da mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya saki, Tambuwal ya isa gidan da karfe 1:30 na rana tare da wasu manyan hadimansa kuma kai tsaye suka shiga ganawar da tsohon shugaban kasan.
Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima
Su biyun sun kammala taron wurin karfe 2:40 na rana kuma ya bayyana cewa sun tattauna ne kan lamurran kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga bisani ya ci abincin rana tare da tawagarsa kuma suka rankaya Masallacin dake cikin OOPL domin yin sallar azahar kafin su bar gidan.
Me suka tattauna a taron?
Channels tv ta ruwaito Bayan fitowa daga taron, Akinyemi, ya bayyana cewa gwamna ya ambata musu cewa tattaunawar ta ta'allaƙa ne kan abubuwan da suka shafi ƙasa.
A wani labarin kuma kun ji cewa Jam'iyyar APC ta lashe zaɓen Ciyamomi 13 da Kansiloli 171 Jihar Ebonyi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ebonyi, ta bayyana APC a matsayin jam'iyyar da ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin 13 na jihar.
Har ila yau, jam'iyyar mai mulki bata sassauta ba, ta samu nasarar kawo dukkan kujeru 171 na kansilolon gundumomin jihar baki daya.
Asali: Legit.ng