An Yi Garkuwa Da Wasu Fitattun Jaruman Fina-Finan Nollywood A Enugu

An Yi Garkuwa Da Wasu Fitattun Jaruman Fina-Finan Nollywood A Enugu

  • Kungiyar jaruman Fina-Finai ta ƙasa AGN ta bayyana cewa tana zargin an yi garkuwa da mambobinta guda biyu a jihar Enugu
  • A wata sanarwa, AGN ta ce iyalan jaruman biyu sun tabbatar da cewa tun da suka fita ɗaukar Fim a garin Ozalla ba su dawo ba
  • Sace mutane da nufin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa na ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaro da ya addabi Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Enugu - Shahararrun Jaruman Fim na masana'antar shirya fina-finai Nollywood kuma mambobin ƙungiyar jarumai AGN, Cynthia Okereke da Clemson Cornel, sun shiga hannun masu garkuwa a jihar Enugu.

Dataktan sadarwa na ƙunguyar AGN, Monalisa Chinda, ita ce ta sanar da haka a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Instagram ranar Jummu'a.

Taswirar jihar Enugu.
An Yi Garkuwa Da Wasu Fitattun Jaruman Fina-Finan Nollywood A Enugu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A sanarwan, Chinda ta bayyana cewa Jaruman biyu sun ɓata ne bayan iyalansu sun tabbatar ba su dawo gida ba daga wurin ɗaukar Fim a garin Ozalla, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

2023: 'Zan Kawo Karshen Yan Bindiga A Zamfara' Atiku Ya Karɓi Jiga-Jigan APC Da Suka Koma PDP

A cewarta, shugaban ƙungiyar AGN na kasa, Emeka Rollas, ya yi kira ga mambobi su guji fita wajen gari ɗaukar Fim matukar ba su samu tabbacin tsaro ba domin tsare kan su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Bayanai sun nuna mambobin ƙungiyar jarumai biyu Cynthia Okereke da Clemson Cornel sun ɓata bayan iyalansu sun tabbatar ba su dawo daga wurin ɗaukar Fim ba a garin Ozalla jihar Ogun."
"Ana zargin jaruman biyu garkuwa aka yi da su kuma hakan ya ƙara jefa tsoro a tsakanin mambobin mu game da tsaron jarumai da ke shirya Fina-Finai a ƙasar nan."
"Duba da wannan cigaban, shugaban ƙungiya na ƙasa, Ejezie Emeka Rollas, ya gargaɗi jarumai su guji fita gefen gari ɗaukar fim har sai sun samu cikakken tsaro da zai kare lafiyar su."

Wane mataki aka ɗauka?

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da wani gwamna sun sa labule da Sanatocin jam'iyyar hamayya a Abuja

Sanarwan, wacce ta bayyana kaɗuwar shugaban AGN, ta roki hukumomin tsaro su matsa da bincike domin kuɓutar da Jaruman cikin ƙoshin lafiya.

Haka zalika ya bukaci abokanan aikin su da su yi wa jaruman Addu'ar Allah ya kubutar da su.

A wani labarin kuma Hadimin Gwamna Sanwo-Olu Na Jihar Legas Ya Rasu A Hadarin Mota

Mai taimaka wa gwamna Babajide Sanwo-Olu kan harkokin ilimi, matasa da dalibai, Mista Sanyanolu ya rasu yau Jumu'a.

Babban hadimin gwamnan ya rasa rayuwarsa ne yayin da Motarsa ta bugi wani ATM a yankin Maryland yana tsaka da zabga gudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262