Tsabar Rashin Kunya: Mallami Ya Fallasa Kwarton Matansa Da Ke Sallah A Masallacin Da Ya Ke Limanci

Tsabar Rashin Kunya: Mallami Ya Fallasa Kwarton Matansa Da Ke Sallah A Masallacin Da Ya Ke Limanci

  • Wani magidanci malamin addinin musulunci, Lukman Shittu ya shaida wa kotu a Ibadan cewa baya sha'awar cigaba da auren matarsa
  • Shittu ya koka kan halin matarsa na bin maza a waje inda ya ce saboda rashin mutunci kwarton matansa ma a masallacin da ya ke limanci ya ke sallah
  • A bangarar matar, ta shaidawa kotu cewa mijinta ba mutumin kirki bane kuma ya kan kawo matan banza har gidansu na aure kuma ya rushe mata jarin sana'a

Ibadan - Wani malamin addini, Lukman Shittu, ya roki wata kotun gargajiya da ke zamanta a Mapo, Ibadan ta raba shi da matarsa saboda bin maza da ta ke yi na bata masa rai, rahoton Daily Nigerian.

Mr Shittu, wanda suka shafe shekaru 20 suna zaman aure da matarsa, ya ce a yanzu bana kaunar matar.

Kara karanta wannan

Matata Sai Ta Karbi Kudi A Hannu Na Kafin Ta Yarda Muyi Kwanciyar Aure, Yarima Ya Fada Wa Kotu

Gudumar Kotu.
Tsabar Rashin Kunya: Mallami Ya Fallasa Kwarton Matansa Da Ke Sallah A Masallacin Da Ya Ke Limanci. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matata ta fara tuka mota bayan ta bar gida na. Ta min karya wai ɗan uwanta ya siya mata amma binciken da na yi ya nuna mutumin da ta ke kwanciya da shi ne ya siya mata.

Ta fara rashin ji ne lokacin da na dena bata kuɗi

Shittu ya fada wa kotu cewa matarsa ta fara nuna halayen da baya so ne a lokacin da abubuwan suka rincabe masa ya kasa bata kudin hayan shago.

"Ta fara dawowa gida latti. Ta dauke yara na uku daga gida na. Ta canja wa ɗan auta na makaranta ba tare da sani na ba, sauran biyun ma ba su dauka na mahaifinsu.
"A watan Ramadan da ta wuce, na gayyaci daya cikin yara na amma ya ƙi zuwa.
"Shin ko ka san cewa masoyin Fisayo yana sallah a masallacin da ke limanci?" Mr Shittu ya koka.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Da kudin budurwa ta tafi dakin saurayi, ya toshe kiran ta yayin da take hanyar zuwa

Martani Fisayo

Tunda farko, Mrs Fisayo, ta ce mijinta ba mutumin kirki bane kuka yana mata barazana.

Ta ce Shittu ya yaudara ta ta karbo bashi daga banki da sunan za ta fara sana'a amma bata san neman mata ya ke yi da kudin ba, har ma yana kawo yan mata gida.

Ta kuma ce ya rusa shagonta da nufin ya hana ta samun kudin kula da kanta.

Hukuncin kotun

Yayin yanke hukuncin, alkaliyar kotu, S.M Akintayo ta raba auren kan dalilin cewa mutanen biyu ba su kaunar juna.

"Domin zaman lafiya, an raba aure tsakanin Shittu da Fisayo daga yanzu.
"Fisayo ta rike yara amma kada a hana Shittu ganin yaransa.
"Zai rika biyan kudin abinci N30,000 duk wata daga watan Yulin 2022," in ji Mrs Akintayo.

Kotun ta kuma bada umurnin kada Shittu ya sake cin mutunci ko barazana ga Fisayo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164