Bidiyon karamar yarinya dake kaunar Sheikh Pantami, ministan ya sha alwashin tuntubar danginta

Bidiyon karamar yarinya dake kaunar Sheikh Pantami, ministan ya sha alwashin tuntubar danginta

  • Wata karamar yarinya mai suna Rukayya ta bayyana a wani bidiyo inda take tabbatar da kaunar da take yi wa Sheikh Ali Isah Pantami
  • Kamar yadda 'yar uwar yarinyar ta sanar, har wasika ta rubuta tare da sa hannu ga ministan kuma an kai ta Masallacin Annoor dake Abuja amma bata samu ganinsa ba
  • Tuni wannan bidiyon ya riski ministan inda ya nuna jin dadinsa da godiyarsa tare da kwarara mata addu'a inda ya tabbatar da cewa zasu tuntubi 'yan uwan yarinyar

Bidiyon wata karamar yarinya wacce aka bayyana sunanta da Rukayya dake kaunar Sheikh Ali Isah Pantami ya bayyana.

A bidiyon da 'yar uwar yarinyar mai amfani da sunan @Miss_Luthor ta saki a shafinta na Twitter tare da janyo hankali ministan ta hanyar kiran sunansa, ta sanar da irin kaunar da yarinyar ke wa ministan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jama'a suna ta mutuwa bayan cin abinci mai guba a wata karamar hukuma

Sheikh Ali Isah Pantami
Bidiyon karamar yarinya dake kaunar Sheikh Pantami, ministan ya sha alwashin tuntubar danginta. Hoto daga @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

A wallafarta:

"Salam, 'yata mai suna Rukayya tana matukar kaunar Sheikh Pantami. Duk lokacin da taji muryarsa a talabijin, a guje take zuwa tana ihun "Sheikh Pantani". Ta rubuta masa wasika kuma ta sa hannu a kai da kanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Daga karshe mun kai ta Masallacin Al Noor amma bata samu ganin Farfesa Isah Pantami ba."

Bayan wallafar da riski ministan a shafinsa na Twitter, yayi martani kamar haka:

"Na yi murnar jin hakan, diyata Rukayya babbar mai sona ce. Abokin aikina zai tuntube ku da izinin Allah. Ina muku fatan alheri. Allah ya amsa dukkan bukatunta, ina godiya kan wasikar da ta rubuta min. Godiya."

Babban Masallaci, Sauran Wuraren da Boko Haram ke Shirin Kai wa Hari a birnin Abuja

A wani labari na daban, babban birnin tarayyar Najeriya na Abuja na fuskantar barazanar tsaro a halin yanzu, ‘yan ta’adda na shirin kai wasu munanan hare-hare.

Kara karanta wannan

Karamar Yarinya ta Cakare Cikin Shigar Amare, Tace Mahaifinta ne Angonta

Rahoto na musamman da Daily Nigerian ta fitar a ranar Talata, 26 ga watan Yuli 2022 ya nuna ISWAP, Boko Haram da ‘yan bindiga su na shirya ta’adi.

Miyagun za suyi yunkurin aukawa makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari, sannan za su iya kai hare-hare a wuraren da ake ibada a Abuja. Jaridar ta ce bayanin da aka samu ya nuna ‘yan ta’addan za su iya aukawa wurin aikin jami’an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng