Da ɗuminsa: Ƴan ta'addan Boko Haram sun buɗewa sojoji wuta kusa da Abuja, wasu sun rasa rayukansu

Da ɗuminsa: Ƴan ta'addan Boko Haram sun buɗewa sojoji wuta kusa da Abuja, wasu sun rasa rayukansu

  • Wasu 'yan ta'addan da ake zargin na Boko Haram ne sun kai wa sojoji dake matsayar su farmaki a kusa da tsaunin Zuma na Niger
  • An gano cewa, sun riska sojojin wurin karfe 7 na yammaci inda suka bude musu wuta na kusan mintuna 30 kafin su arce
  • Majiya ta tabbatar da cewa, sun tsere zuwa kan hanyar jihar Kaduna tun kafin isowar sojoji daga barikin Zuma

Zuma Rock, Niger - Wasu sojoji sun rasa rayukansu yayin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai musu farmaki a matsayar sojojin dake kusa da tsaunin Zuma a jihar Niger a daren Alhamis.

Yankin yana kusa da garin Madalla, mitoci kadan daga Zuba kan babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Martanin gaggawa: Sojoji sun sheke tsageru 30 da suka kai kan jami'an fadar Buhari

Farmakin Sojoji
Da ɗuminsa: Ƴan ta'addan Boko Haram sum buɗewa sojoji wuta kusa da Abuja, wasu sun rasa rayukansu
Asali: Original

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, maharan sun isa wurin mintoci kadan kafin bakwai na yammaci ta cika kuma suka budewa sojojin wuta a take.

"Sun karbe ikon yankin na wurin mintuna 30 kuma suka cigaba da harbe-harbe kafin su nausa kan babbar hanyar Kaduna," majiya tace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan kusan mintuna 20 da 'yan ta'addan suka bar wurin, sojoji daga barikin Zuma sun garzayo wurin da lamarin ya faru sannan suka kwace ikon wurin.

Tawagar sintiri ta jami'an 'yan sanda sun hallara a wurin da lamarin ya faru.

Karin bayani nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng