Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari

Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari

  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da fatattakar wasu 'yan ta'adda da suka kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja
  • An samu tsaiko a makon nan yayin da 'yan ta'adda suka farmaki sojojin da ke aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • A rahotannin baya, san samu wani bidiyon da ke yawo yana cewa, 'yan ta'adda sun yi barazanar kai hare-hare Abuja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da ragargazar wasu 'yan ta'adda 30 da ake zargin sun kai hari kan sojojin fadar shugaban kasa a makon nan.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja, inda aka hallaka jami'ai uku tare da jikkata wasu.

Daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana aikin da jami'an suka yi a wani taron manema labarai na mako bibbiyu kan ayyukan tsaro a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Duk sace N109bn na kasa, kotu ta ba da belin akanta janar da shugaba Buhari ya dakatar

Yadda sojoji suka hallaka 'yan ta'adda a Abuja
Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai wa sojoji hari | Hoto: thecable.ng
Asali: Twitter

Da yake bayyana jaruman dakarun da suka yi aiki, Mista Onyeuko ya ce dakarun 7 Guards Battalion da na 167 Special Force Battalion ne suka yi da aikin tare da rundunar sojin sama na “Operation Whirl Punch”".

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, ya ce sun yi aikin ne tsakanin ranakun Lahadi zuwa Talata na wannan makon.

Ya kuma bayyana cewa, sojojin sun yi nasarar kakkabe kauyukan Kawu da Ido daga fakewar 'yan ta'adda tare da lalata maboyarsu da kurminsu.

A cewarsa, sojojin na kasa sun kuma kwato babura shida, bindigogi kirar AK47 guda biyu, daya cike da mujalla ta LMG da dai sauran su a lokacin da ’yan ta’addan suka yi artabu da jami'ai, rahoton TheCable.

A kalamansa:

“Shugaban rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro na fatan sake tabbatar wa ‘yan Najeriya jajircewarsu da tabbatar da amincin dukkan ‘yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buhari zai sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

Hakazalika, ya tabbatarwa 'yan Najeriya komai ya komai daidai a birnin, kuma kowa zai iya komawa harkokinsa na yau da kullum.

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai hari kan motar kudi, sun hallaka ma'aikacin banki

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta ce an kashe wani jami’in banki, biyo bayan wani hari da aka kai kan wata motar kudi a jihar, The Cable ta ruwaito.

Geoffrey Ogbonna, kakakin rundunar ‘yan sandan Abia ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba 27 ga watan Yulin 2022.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai harin ne a ranar Talata a mahadar Ntigha, kusa da Umuahia, babban birnin Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.