Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 30 a Abuja - Hedikwatar Sojoji

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 30 a Abuja - Hedikwatar Sojoji

  • Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarun ta sun kashe yan ta'adda 30 tare da lalata maboyar su a birnin Abuja
  • Dakarun 7 Guards Battalion da hadin gwiwar rundunar sojin sama sun gudanar da sintiri a yankin Bwari tsakanin 24 – 26 ga Yuli 2022
  • A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka kashe sojoji guda shida a wani harin kwantan bauna da suka kai wa sojoji a Abuja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kakakin DHQ, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na mako-mako kan ayyukan sojoji da nasarorin da aka samu a atisayen da suke gudanarwa a duka yankunan kasar. Rahoton 21STCENTURYCHRONICLES

Ya ce dakarun 7 Guards Battalion da 167 Special Force Battalion tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama na Operation WHIRL PUNCH sun gudanar da sintiri a yankin Bwari a tsakanin 24 – 26 ga Yuli 2022.

Kara karanta wannan

Martanin gaggawa: Sojoji sun sheke tsageru 30 da suka kai kan jami'an fadar Buhari

Janar Onyeuko ya ce,

MILITARY
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 30 a Abuja - Hedikwatar Sojoji FOTO Legit.NG
Asali: Twitter
“Sojoji sun yi nasarar magance matsalar tsaro a kauyukan Kawu da Ido.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Bayan haka, an kashe ‘yan ta’adda kusan 30 tare da lalata maboyarsu yayin da sojojin kasa suka kwato babura 6 x, bindigu AK47 guda 2, da Mujallar Harsashi LMG guda 1 x da sauran su.

A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka kashe akalla jami’an sojoji shida a wani harin kwantan bauna da suka kai a kusa da makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Bwari Abuja sa’o’i bayan da suka yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Nasir El-Rufai da wasu manyan jami’an gwamnati.

An kai harin ne a daren Lahadin da ta gabata, kuma kakakin rundunar ‘yan sandan, Kyaftin Godfrey Anebi Abaakpa ya tabbatar da hakan.

Guards Brigade wato Rundunan kare shugaban kasa ta sojojin Najeriya ke da alhakin kare shugaban Najeriya da kare babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

An Yi Jana’izar Daya Daga Cikin Sojojin Da Yan Bindiga Suka Kashe A Abuja, Hotuna

An zabo jami’an da aka kashe ne daga 7 Guards Brigade da ke barikin Lungi, Maitama Abuja.

Rashin tsaro: Mun inganta Matakan tsaro a Abuja – ‘Yan sanda

A wani labari kuma, Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa ta kara baza jami’anta a babban birnin tarayya Abuja, bayan rahotannin hare-haren da aka kai wasu sassan birnin. Rahoton Premium Times

Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Legit.NG ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa