Ku kiyayi Abuja, akwai matukar hatsari a cikinta: 'Dan majalisa ya gargadi abokan aikinsa
- Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Ndudi Elumelu, yayi kira ga abokan aikinsa da su kiyayi zaman Abuja
- Ya shawarci 'yan majalisar da su koma mazabunsu sakamakon tsanantar rashin tsaro a fadin babban birnin tarayyan
- Sai dai tuni mataimakin kakakin majalisar ya taka masa birki inda ya ja kunnensa kan siyasantar da rashin tsaron kasar nan
FCT, Abuja - Shugaban marasa rinjaye na majlisar wakilan Najeriya, Ndudi Elumelu, yayi kira ga abokan aikinsa da su kiyayi Abuja a yayin dogon hutunsu sakamakon halin da tsaron kasar nan ke ciki.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Elumelu ya sanar da hakan ne a ranar Laaba yayin da mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase, ya sanar da cewa majalisar za ta tafi hutu har zuwa ranar 20 ga watan Satumba.
Ba za ta sabu ba: Kungiyar kiristoci ta fara yaki da ci da addini, za ta ba da katin shaida ga malamai
"Ina son rokon mambobinmu, Abuja a yanzu ba lafiya, don Allah idan zai yuwu ku koma mazabun ku. Wurin akwai rashin tsaro," yace.
Tsokacin Elumelu ya zo ne bayan mazauna babban birnin tarayyan suna fama da tsoron cigaban ta'addancin da ya fara kunno kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin kwanakin nan, gwamnati ta yi umarnin rufe makarantun babban birnin tarayyan.
A ranar Juma'a da ta gabata, 'yan ta'adda sun kai farmaki kan wasu sojoji masu tsaron fadar shugaban kasan. An rasa rayukan sojoji takwas a mummunan farmakin.
Hakazalika, a watan Yulin, 'yan ta'adda sun kai mummunan farmaki magarkama ta Kuje dake babban birnin tarayyan, inda suka saki daruruwan 'yan gidan har da 'yan ta'addan Boko Haram.
A martanin mataimakin kakakin majalisar kan tsokacin Elumelu, Idris Wase wanda ya jagoranci zamani majalisar, ya ja kunne shugaban marasa rinjayen da kada ya saka siyasa a harkar tsaro.
Batun rashin tsaro: Sanatocin Najeriya sun hado kan shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, suna ganawa
Ya bayyana cewa irin wannan tsokacin na iya fatattakar masu saka hannayen jari a kasar nan.
"Tsaro matsalar kowa ce kuma kada mu siyasantar da tsaro. Ina rokonmu da cewa duka ya kamata mu hada kai, mu yi aiki tare kuma mu yi tunanin ta yadda zamu hada kai wurin shawo kan matsalar."
Wani abu mai fashewa ya tashi a ofishin gwamnatin jihar Kogi
A wani labari na daban, wani gagarumin karar fashewar abu ya tashi a farfajiyar ofishin sakataren gwamnatin jihar Kogi, Dr. Folashade Arike Ayoade.
Ofishin shi ne kusa da Lugard Street. inda majalisar zartarwar kungiyar 'yan jaridan Najeriya, reshen jihar Kogi yake, jaridar Punch ta ruwaito.
Karar fashewar abun an ji shi wurin karfe 8:30 na safiyar Talata yayin da 'yan jarida suka taru domin shirin ayyukansu na ranar.
Asali: Legit.ng