Lalacewar Naira: Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan CBN yayin da dala ta kai N700
- Yayin da farashin Naira ke kara durkushewa a duniya, majalisar dattawa ta shirya daukar matakin gaggawa
- Majalisar dattawa ta nemi ganin gwamnan babban bankin Najeriya domin sanin dalilin rugujewar farashin Naira
- Tun farkon mulkin shugaba Buhari Naira ke fuskantar matsanancin yanayi na rage daraja, lamarin da ke kara dagula tattalin arzikin Najeriya
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan faduwar darajar Naira.
Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi (APC, Ekiti ta Arewa) ya gabatar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu dai darajar Naira bai wuce tsakanin N690 zuwa N700 ba kan kowacce dala a kasuwanni.
Da yake bayar da gudunmawa a muhawara kan kudurin, sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce Naira za ta kara daraja idan muna cin abin da muka noma.
Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A nata bangaren, Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi, ta zargi CBN da laifin duk wani lamari na rushewar darajar na Naira.
A cewarta:
"Yawancin abin da ke faruwa shi ne saboda mutane suna fitar da dala suna sayar da su suna dawo da su - ya kamata mu ladabtar da wani kan abin da ya faru da darajar Naira.
“Lokaci ya yi da za mu duba gaba daya abin da ke faruwa. Abin da ke faruwa da dala, kwatankwacin abin da ke faruwa ne ga Najeriya.”
Majalisar dattawan ta bukaci babban bankin kasar da ya dakatar da faduwar darajar Naira cikin sauri, rahoton Vanguard.
An amince da kudirin gayyato gwamnan ne bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya amince da hakan.
Sanatoci sun bai wa Buhari wa'adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro, sun yi barazanar tsige shi
A wani labarin, mambobin majalisar dattawa daga jam'iyyun hamayya sun baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wa'adin mako shida ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Channels TV ta ce sun yi barazanar fara bin matakan tsige shugaban ƙasan idan ya gaza shawo kan matsalar tsaro a cikin wa'adin da suka ɗibar masa.
Shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda, shi ne ya bayyana matsayar Sanatocin yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng